A ‘kalla mutane 30 zuwa 60 Yan fashi Daji suka kashe a saban harin da suka Kai a Garin goronyo Wanda Hakan yafusata Shugaban kasar Nigeria Muhammad Buhari Wanda yaci al-washin.

A 'kalla mutane 30 zuwa 60 Yan fashi Daji suka kashe a saban harin da suka Kai a Garmin goronyo Wanda Hakan yafusata Shugaban kasar Nigeria Muhammad Buhari Wanda yaci alwashin.

Ƴan uwa da abokar arziƙin mutanen nan 30 zuwa 60 da suka gamu da ajalinsu yayin wani harin ƴan fashin daji a garin Goronyo da ke jihar Sokoto na ci gaba da jimamin rashin ƴan uwan na su.

A safiyar yaune mukasamu saban rahotan daga shafin BBC hausa Wanda rahotan kecewa wasu mugayan Yan fashi Dani sun Kai Hari Cikin kasuwa Wanda Wanda suka kashe mutane akalla mutum 30 Zuwa 60 acikin kasuwar.

BBC ta tattauna da wasu mazauna garin, inda suka bayyana halin da suka shiga, a lokacin da mahran suka yi wa garin kofar rago tare da buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Wani mutum da muka sakaye sunansa, ya ce bai taba ganin tashin hankali a rayuwarsa irin wannan ba, domin ta kai hatta katangar gidan da yake tana jijjiga saboda yadda harbi ya karade gari ko ta ina.

“Ina zaune tare da mutane kawai sai muka ji ana barin wuta, aka ce ai ɓarayi ne, karfe 4:30 na maraice, daga nan kuma muka tashi muka ruga da gudu, muka tsallake katanga muka fada wani gida, ko ina barin wuta ake, ba su tafi ba sai ƙarfe shidda, sannan suka hau baburansu suka wuce.

A cewar wannan mutumin, Allah ne kawai bai sa kwanansa ya ƙare ba, amma ba don haka ba da tuni shi ma yana cikin mutanen da suka mutu.

”Bayan sun tafi ko da na fito sun kashe mutum mutum hudu a bayan gidan da na ɓuya, duka gari dai ya ruɗe kowa yana biɗar ƴan uwansa, abin dai babu daɗin gani ko kadan” inji wannan shaida, a zantawarsa da BBC Hausa.

Shi ma wani shaida da muka sakaye sunansa da ke zaune a garin na Goronyo, ya ce kasuwar garin da aka kai harin bata taba cika tun da aka fara damuna kamar ranar da aka kai wannan farmaki da ya janyo mutuwar kimanin mutane 50 ba.

”Ina kusa da asibiti ban ji komai ba sai karar bindiga na tashi, ashe sun kewaye ko ina, da jin haka kuwa sai kowa ya kama gabansa, haka muka yi ta kutsawa gidajen matan aure, sai ka ga muum 20 a dakin matar aure, kuma a gaji a kulle haka nan” inji shi.

A cewarsa ‘an kashe mutum 7 cikin ƴan kato da gorar da suka yi kokarin tunkarar ‘yan fashin dajin domin dakile su kafin su far wa jama’ar gari da suke kokarin tunkara.

Shi dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce lokaci na gab da zuwa ƙarshe ga mummunar ɓarnar da ‘yan fashin fashin daji ke haddasawa musamman a yankin arewacin ƙasar.

Muhammadu Buhari na wannan jawabi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar don juyayin mummunan harin da aka kai kan kasuwar Goronyo wadda ta cika maƙil, inda majiyoyi ke cewa an kashe kimanin mutum 30 zuwa 60 yayin harin na ranar Lahadi.

Ya dai yi kira ga ‘yan ƙasar da kada su karaya, maimakon haka su ci gaba da haƙuri don kuwa hukumomi sun duƙufa fiye da kowanne lokaci a baya wajen kare ‘yan Najeriya da kuma murƙushe gungun masu ɗauke da makamai.

To jama’a kucigaba da kasancewa tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews Domin samin labaran Duniya kaitsaye.

KU KARANTA WANNAN

Alamo Ya Nuna Cewa Aminan Juna Biyu Jarumai Kannywood Sun Kamu Da Son Hamisu Breaker Dorayi

Waddannan sune jihohin da biyan malaman makaranta albashinsu, jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Lagos, Ekiti Wanda Hakan yajowo musu

Subahanallah: Wata yarinya mai suna Bilkisu badamasi ta bayyana yadda mahaifinta yake lalata da ita cikin dare

Kalli Halin Da Sarkin Bagudu Ya Kasance Bayan Kubutarsa Daga Hannun ‘Yan Ta’adda Masu Garkuwa Da Mutane

Bayyanar Wani Bidiyo Na Adam A Zango Da ‘Yarsa Ya Dauki Hankalin Mutane

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button