Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I ya yabawa dakarun tsaron bisa kashe ‘yan fashin dajin.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I ya yabawa dakarun tsaron bisa kashe ‘yan fashin dajin.

An kashe ‘yan fashin daji 10 a wasu guraren da ke fama da rikici a jihar Kaduna.

Gamayyar dakarun tsaro sun yi arangama da ‘yan fashin dajin dauke da muggan makamai a Kwanan Bataru dake wajen garin Fatika a Karamar Hukumar Giwa kuma suka yi taho mu gama.

Cikin wata sanarwa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, yace daidai lokacin da ake musayar wuta, an kashe ‘yan fashin dajin su 10 yayin da wasu dayawa suka tsira da raunukan bindiga.

Ya kara da cewa ‘yan fashin dajin wadanda suka samu tserewa sun gudu sun bar babura dayawa da bindiga daya da wayoyin hannu da fitulun tocilan da kuma wasu layu.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I ya yabawa dakarun tsaron bisa kashe ‘yan fashin dajin. Gwamnan ya yiwa dakarun fatan alkhairi da samun nasara a ayyukan da suke gudanarwa a jihar.

To jama’a zamuso mu karbi ra’ayoyinku na salon jinjinawa dakarun sojojin Jihar Kaduna da Kuma tayin murna ga gwamnan jihar.

Kada kumanta a harkulum Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN:

 

A ‘kalla mutane 30 zuwa 60 Yan fashi Daji suka kashe a saban harin da suka Kai a Garin goronyo Wanda Hakan yafusata Shugaban kasar Nigeria Muhammad Buhari Wanda yaci al-washin.

Bayani akan wasu jaruman kannywood Mata wanda suka kasance ba hausawa ba

 

Waddannan sune jihohin da biyan malaman makaranta albashinsu, jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Lagos, Ekiti Wanda Hakan yajowo musu

 

To jama’a kada KU gaji damu ku daure ku dannamana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button