Advertisement

Jarumi kuma Darakta Falalu a dorayi yayi zazzafan martani ga shuwagabannin kasar nan akan kashe mutane da ake jihar Sokoto

Jarumi kuma Darakta Falalu a dorayi yayi zazzafan martani ga shuwagabannin kasar nan akan kashe mutane da ake jihar Sokoto

Kamar yadda muka sami wannan labarin: a shekaran jiya ne ranat Lahdi da misalin karfe hudu 4 da ‘yan mintuna ‘yan bindiga suka kai wani mummunan hari a kasuwar goronyo dake jihar sakkwato, inda suka kashe mutane da dama sannan kuma suka raunata wasu.

Sannan kuma ‘yan bindigar sun yiwa mutane asarar dukiyoyi masu tarin yawa, bayan faruwar wannan al’amarin sai ficaccan jarumi kuma darakta a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood Falalu a dorayi, yayi martami ga shuwagabanni akan abubuwan da suke faruwa ga talakawa da kuma mummunan halin da suke fadawa.

Jarumi Falalu a dorayi ya wallafa wannan martanin nasa ne cikin wani rubutu a shafinsa na sada zumunta instagram, inda ya fara da cewa.

Kalmomi guda 2.

Hakki da Amana.

Suna da nauyi da kowa sai an masa tambaya a mansu, tsakanin mutum da iyalin sa, ‘yan uwansa, makotansa, abokansa.

Sai babban nauyi mafi girman bala’i wato mulki, ko yaushe masu mulki zasu farka suyi tunanin farin tuhumar rayuka da dukiyar al’umma da suka salwanta sabida sakaci da son zunciya, tuhuma ce dake jiran duk mai mulki tun daga zamansa a kabari har zuwa tashin alkiyama.

Akwai mamaki da takaici duk da ance an zuba matakan tsaro a Sokoto da Zamfara amma a shiga kasuwar Garanyo a kashe rai sama da hamsin 50, a kore shabu da tumakai a kone gurin sana’a da abubuwan hawan al’umma, kuma duk lokutan da aka dauka anayi Gwamnati da jami’anta basu zo ba, to ai shikenan.

Idan bukatar kansu ce sukan tara jami’an tsato da bindugu kai kace yakin duniya na uku 3 za’a yi, mun gani kwanannan a zaben Local Government da zaben shugaban jam’iyya amma ana kashe Yara, Mata, Tsofaffi, Magidanta, sannan ayiwa mata fyade a kone gidaje da dukiyoyi, ina alkawarin da kuka dauka.

Muna rokon Allah Jallah wa Alah yadda akayi addu’a ruwan sama sa dawo Allah ka kawo mana karshen wannan rashin imanin, duk wanda yake da hannu a ciki ko ya sani yaki magana Allah ka tona asirin su Ameen, Ya Hayyu Ya Qayyum.

Karanta wannna labarin.

Bayani akan wasu jaruman kannywood Mata wanda suka kasance ba hausawa ba

Karanta wannan labarin.

Hassada Ce Tasa Ake Tsinewa Rahama Sadau Idan Tayi Abunda Bai Dace Ba Cewar Wani Jarumi A Kannywood Abdullahi Amdaz

Karanta wannan labarin.

Alamo Ya Nuna Cewa Aminan Juna Biyu Jarumai Kannywood Sun Kamu Da Son Hamisu Breaker Dorayi

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button