Advertisement

Jatumar kannywood mai fitowa a shirin Dadin kowa Stephanie ta bayyana dalilin da yasa take rera wakokin yabon Annabi Muhammad S.A.W

Jatumar kannywood mai fitowa a shirin Dadin kowa Stephanie ta bayyana dalilin da yasa take rera wakokin yabon Annabi Muhammad S.A.W

Shahararriyar jarumar cikin shirin Dadin kowa mai dogon zango wanda tashar Arewa24 take haskawa a duk mako, Sarah Aloysius wacce aka fi sani da Stephanie, ta bayyana cewa matukar girmamawa da takewa Annabi Muhammad (S.A.W) ne yasa aka ganta tana rera wakokin yabon sa cikin harshen larabci a cikin wata bidiyo a shafin sada zumunta.

Jarumar wacce ta kasance ‘yar addinin kirista ce ita ma ta kasance a cikin miliyoyin al’ummar musulmai na duniya domin gudanar da bikin maulidin Annabi Muhammad (S.A.W), duk data kasance addininta ya sha babban dana musulmai.

Yayin da Hausadaily time ta ruwaito cewa, lokacin da jaruma Stephanie take zantawa da Sahelian time ta bayyana cewa, tana da tarin wasu wakoki na Larabci na yabon Annabin musulmai Muhammad Rasulullah (S.A.W).

Jarumar ta kara da cewa, tana sauraran wakokin a duk lokacin da take tukin mota ko kuma tana gida a zaune, tace na fara jin wakar ne daga wani abokin aiki na kuma nan da nan naji wakar ta kwantamin na roki shi daya tura min, nan kuwa naci gaba da sauraran wakar har saida na iya rerawa.

Stephanie ta kara da cewa: Bidiyon yaja hankalin jama’a da dama wasu na zagi wasu kuma suna nuna goyon baya, a matsayina na kirista nayi imani zan iya coci na rera wakokin yabo kamar yadda nake yabon Yesu sabida girmamawa da nake masa, amma da yawa sun bayyana abin da nayi a matsayin kamar na wanda ke neman suna a kafafan sada zumunta.

A lokacin da aka tambayi Stephanie ko abin data aikata hanyace ta karfar Musulinci a matsayin addini sai jarumar tace, wadanda suke min fatan alkairi suci gaba da yimin addu’ar fatan alkairi, domin Allah ne kadai yasan abin da yafi dacewa da rayuwar mu.

Ta kara da cewa: Na girma a garin Maiduguri kuma a lokacin dana girma nayi hulda da mutane wanda suke addinai daban-daban, sannan kuma an koyar dani na girmama addinin mutane, har yanzu muna iya kasancewa da addinai daban-daban kuma har yanzu muna zaune tare da juna cikin aminci da jituwa.

Duk Musulman duniya suna murna da zagayowar ranar haihuwar Annabin Musulinci Muhammad Rasulullah (S.A.W), a duk wata na uku 3 na kalandar Musulinci Rabiul Auwal.

Karanta wannan labarin.

Yadda jaruman masana’antar kannywood Maza da Mata suka kai ziyarar bazata ga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Karanta wannan labarin.

Cikakken Bayyana Game Da Bayyanar Babbar Yar Shugaban Kasa Hadiza Buhari Tare Da Iyalanta

Karanta wannan labarin.

Matashi Ya Tsinchi Naira Miliyan 25 An Bashi Kyauta Naira Miliyan 5 Ladan Tsintuwa

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button