Trending

Matashi Ya Tsinchi Naira Miliyan 25 An Bashi Kyauta Naira Miliyan 5 Ladan Tsintuwa

Matashi Ya Tsinchi Naira Miliyan 25 An Bashi Kyauta Naira Miliyan 5 Ladan Tsintuwa

Kamar Yadda Kuka Sani A Yanzu Yadda Mutane Suke Cikin Wani Hali Na Kunchi Da Talauchi, Wanda Hakan Ne Yasaka Wasu Suke Bin Wasu Hanyoyi Da Basu Dace Ba Domin Su Samu Kudin Da Zasuyi Rayuwa.

Wannan Labarin Wani Saurayine Daya Tsinchi Tsabar Kudi Dalar Amurka ($50,000) Wanda Kimanin Miliyan Ashirin Da Biyar A Kudin Nigeria, Kuma Ya Nemi Masu Kudim Ya Basu, Yadda Su Kuma Sukaji Dadin Wannan Al’amari Suka Bashi Kaso Daya Cikin Biyar Wato ($10,000) Kimanin Miliyan 5 A Kudin Nigeria.

Mun Samo Asalain Labarin A Global News 24 Yadda Rohoton Ya Fara Kamar Haka.
AKWAI DARASI ANAN

Daga Kasar Liberia Matashi Emmanuel
Tuloe ya tsinci kudi dalar Amurka dubu
hamsin ($50,000) kimanin Naira Miliyan
25, bayan ya tsinci kudin sai bai rike ba,
yabi diddigi ya mayar wa mai kudin
abinsaLabarin matashin ya yadu sosai a duk
manyan kafofin watsa labarai na duniya
ba iya Kasar Liberia ba, akwai masu son
zuciya da suke ganin wai matashin yayi
wauta da ya tsinci wadannan makudan
kudade ya mayar.

Shugaban Kasar Liberia George Weah ya
sa an kira matashin domin ya jinjina
masa, sannan ya bashi kyautar kudi dalar
Amurka dubu goma ($10,000) kimanin
Naira Miliyan 5.

Shugaban Kasar Liberia bai barshi haka
ba, ya bashi kyautar mashina guda 2,
sannan ya dauki nauyin karatunsa har
zuwa matakin digiri na biyu, kuma duk
wata za’a bashi albashin dalar Amurkadari biyar ($500) kimanin Naira dubu
dubu dari biyu da hamsin Darasi, a rayuwa duk abinda ka sameshi
ta hanyar haram inda zakayi hakuri kabi
ta hanya mai kyau, ka nema ta hanya mai
kyau, sai Allah Ya baka ta hanyar halal.

Inda wannan matashin bai mayar da
kudin ba, kudin ba zai taba masa albarka
ba, zai kama hanyar shashanci ya fara
hulda da karuwai, karuwa zata jashi su
kashe kudin a hotel, tsanani shekara
guda kudin ya kare, yanzu da yayi hakuri
ya samu mafi alherin abinda ya tsinta yamayarMuna fatan Allah Ya bamu halal, Ya
nesanta haram daga garemu Ameen.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Abun Alfahari Da Wannan Saurayi Yayi.

Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Shikenan Ansaki Bidiyon Tsiraichi Na Mawakiya Tiwa savage

Ku Karanta Wannan Labarin:

Mawakiyar Da Take Fuskantar Bacin Suna Bayan Bullar Bidiyonta Na Iskanchi – Tiwa savage


Ku Karanta Wannan Labarin:

Allah Yasa Hajiya Rabi Kwana Casa’in Tayi Wuff Dani Cewar Balarabe Wambai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button