Shugaban kasa Muhammad Buhari ya Taya tsohon Shugaban kasar Nigeria yakubu gowon murnar cika shekara 87 Wanda Hakan Yasa tsohon Shugaban kasar ya.
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya Taya tsohon Shugaban kasar Nigeria yakubu gowon murnar cika shekara 87 Wanda Hakan Yasa tsohon Shugaban kasar ya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon murnar cikarsa shekaru 87 a duniya.
Shugaban, a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Garba Shehu, ya taya tsohon shugaban kasar da iyalansa murnar da fatan karin lafiya da karfin gwiwa don ci gaba da yiwa kasa hidima.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wata ziyarar aiki ta wuni biyu zuwa Najeriya daga jiya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa wacce babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu, ya fitar a jiya.
Tare da rakiyar Uwargidan Shugaban kasa, Emine Erdogan, Shugaba Erdogan ya shigo daga Angola, sannan zai tashi zuwa Togo a karshen ziyarar tasa.
A yayin ziyarar, ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su duba yarjejeniyoyin fahimtar juna tsakanin kasashen.
To jama’a zamuso mukarbi ra’ayoyinku akan wannan ziyarar tashugaban kasa Amma kafin wannan idan wannan shine karanka nafarko a wannan site din munaso kadaure ko kudaure KU Danna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.
KU KARANTA WANNAN:
Yanzu Aka Saki Sakamakon Jarrabawar Scince And Technical Schools Board Kano State
Ku cigaba da kasancewa da shafin Dalatopnews Domin samin labaran Duniya
2 Comments