Ali Nuhu Yayiwa Jaruma Amal Umar Wasu Kalamai Masu Daukan Hankali Bayan Wallafa Wasu Hotuna Nata Na Birthday

Kamar Yadda Wasu Suka Sani A Jiyane Jarumar Fina-finan Hausa Amal Umar Ta Cika Shekara 23 Da Haihuwa, Yadda Har Mukaga Hotunan Nata Yayi Ta Yawo A Kafafen Sada Zumuntar Zamani Instagram Da Facebook.
Bayan Jarumar Tayi Murnar Ganin Cikarta Shekara 23 A Duniya Sai Da Tayi Wata Addu’a Dayakamata Kowacce Mace Mai Hankali Tayi.
Jarumar Ta Bayyana Cewa Kamar Yadda Taga Ranar Birthday Dinta, Allah Ya Nuna mata Ranar Aurenta.
Sai Dai Wannan Kalami Nata Yayi Matukar Birge Mutane Sosai Ganin Cewa Ta Fadi Wani Abu Sabanin Abunda Ake Ji Daga Bakin Matan Kannywood, Domin Kuwa Da Wuya Matan Kannywood Suna Furta Zancen Aure Idan Ba Tambayarsu Akayi Ba, Sai Kuma Mukaga Jarumar Ta Fadi Wadannan Kalaman Masu Birgewa..
Jarumi Ali Nuhu Ya Wallafa Hoton Amal Umar Tare Dayin Wata Addu’a Da Cewa Allah Ya miki Albarka ‘Yata Kuma Ina Tayaki Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarki, Sannan Allah Ya Kawo Miki Miji Nagari.
Ga Wata Bidiyo Da Mukaci Karo Da Ita Daga Tashar Kundin Shahara Akan YouTube Yadda Sukayi Cikakken Bayani Game Da Hakan.
Toh Dama Haka Ake so Allah Yakawowa Duk Wata ‘Ya Mace Musulma Miji Na Gari Domin Suyi Rayuwar Aurensu Lafiya.
Zamu so Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbij Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannnan Labarin:
Adam A Zango Ya Koka Kan Yadda Ake Zagin Masu Maulidin Manzon Allah S A W
Ku Karanta Wannan Labarin:
Ku Karanta Wannan Labarin:
Jerin shekarun wasu daga cikin jaruman kannywood maza da mata guda 20 wanda kowa yayi mamakin su