Advertisement

Ashe wannan dalilin ne yasa ake zagin mutanen da suke gudanar da maulidi idan shekara ta zagayo

Ashe wannan dalilin ne yasa ake zagin mutanen da suke gudanar da maulidi idan shekara ta zagayo

Kamar yadda kuka sani a kowacce shekarar zagayowar ranar haihuwar fiyayyan halitta Annabi Muhammad (S.A.W), akan gudanar da maulidi daga garuruwa daba-daban domin nuna murna na zagayowar ranar haihuwar fiyayyan halitta Annabi Muhammad (S.A.W.).

Sai dai kowanne gari da irin yadda suke gudanar da nasu maulidin wasu suna fitowa maza da mata suna zagaye akan titi, wasu kuma a zaune suke gudanar da nasu.

Amma akan sami sabani wani lokacin dangane da yadda wasu suke gudanar da nasu maulidin domin suna aikata abunuwan da basu dace ba, sabida sukan hada maza da mata waje daya suna rawa tare da yin wake-wake wanda a wannan lokacin za’a iya samin namiji ya rabi jikin mace, wanda hakan ba dai-dai bane ga ‘yayan musulmai.

Haka kuma akan sami yawan cece-kuce a duk lokacin da shekarar maulidi ta zagayo domin wasu na fadin yin maulidin baby kyau domin Manzon Allah (S.A.W) bai yi ba, inda wasu suke cewa ya halatta domin nuna taya murna ne na zagayowar ranar haihuwar fiyayyan halitta Manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W).

Sai kuma a yanzu mukaci karo da wata bidiyo wanda irin wadannan bidiyoyon ne suke janyowa cece-kuce da abin fadi a duk lokacin da shekarar maulidi ta zagayo, inda zakuga a cikin bidiyon mata da maza ne suke rawa akan titi wanda shigar da matan sukayi shigace wacce bata dace ba domin duk surar jikin su a waje take, kamar yadda zaku gani cikin bidiyon.

Wannan bidiyon munci karo da ita ne a tashar Kundin shahara inda suka wallafa ta domin al’umma sugani su san irin wadannan mutanen ne suke janyowa ake haramta yin maulidi, domin abin da suke bai dace ba idan kuka kalli bidiyon.

Ga bidiyon nan sai ku kalla kai tsaye.

Karanta wannna labarin.

Babu masana’antar shirya fim a duniya da takai kannywood tsafta, cewar sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale

Karanta wannan labarin.

Rawar Iskanchi Da Juya Duwawu Da Rahama Sadau Tayi Ya Janyo Cece – Kuce

Karanta wannan labarin.

An bankado jerin wasu jaruman kannywood mata wanda suka tsufa ba tare da sunyi aure ba

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button