Innalillahi An Kashe Shi Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Wurin Zagayen Maulid A Garin Mararraba/Nyaya

Innalillahi An Kashe Shi Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Wurin Zagayen Maulid A Garin Mararraba/Nyaya

Kamar Yadda Muka Sami Daga Shafin Daily News Hausa Sun wallafa Cewa Mai Gidancin Matashi Ya Rasa Ransa A Ranar Talatar Da Ta Gabata Sakamakon Burma Masa Wuka A Kirji Da Wani Matashi Yayi A Yayin Da Ake Kan Zagayen Maulidi Domin Murna Da Zagayowar Ranar Da Aka Haifi Annabi (S A W) Garin Mararraba /Nyaya Wato Iyakar Abuja Da Jihar Nasarawa

Mamacin Mai Suna Muhammad Sani Wanda Dan Agaji Ne Kuma Yana Aikin Banga Tare Da Yin Saukale A Kasuwar Yan Lemo Dake Garin Mararraba /Nyaya Ya Gamu Da Ajalin Nasa Ne Jim Kadan Da Isowar Sa Bakin Hanya Inda Dandazon Al’ummar Musulmai Ke Zagayen Maulidin Bayan Dan Acaban Da Ya Dauko Sa Ya Saukeshi

Bayan Muhammad Sani Wanda Ya Rasa Rasu Ya Bar Mata Daya Da Ciki (Haihuwa Ko Yau Ko Gobe) Ya Tsallako Titi Domin Shiga Cikin Dandazo Masu Zagayen Maulidin ,Inda Shigar Sa Cikin Jama’a Ke Da Wuya Sai Ya Ga An Biyo Wani Matashi Ana Zarginsa Da Satar Waya Inda Yana Rike Matashin Kawai Sai Ya Fallo Wuka Ya Daba Masa A Kirji Inda Nan Take Ya Zube A Kasa Shi Kuma Barawon Ya Shiga Cikin Rububin Mutane Ya Gudu

Saide Abunda Ya Daurewa Jama’a Kai Game Da Lamarin Shine Yadda Matashin Da Yayi Kisan Ya Sha Duk Da Cewa A Cikin Dandazon Al’umma Ya Aikata Wannan Ta’asar

Saide A Yayin Jin Ta Bakin Jami’an Tsaro Kakakin Yan Sanda Mararraba Ya Tabbatar Da Aukuwar Lamarin Inda Ya Kara Da Cewa Suna Neman Wanda Ya Aikata Laifin Ruwa A Jallo Duk Da Cewa Yayi Layar Zana Inda Da Zarar Sun Cika Hannu Da Shi Zai Fuskanci Hukunci Daya Kamace Shi

Ku Kara Karanta Wannan Labarin

Nasir Ahmad El-Rufai na Jihar Kaduna ya shawarci gwamnatin Najeriya ta dauki matasa 1,000 daga kowace karamar hukuma aikin bayar da tsaro a Nigeria Wanda Matasan Sunyi magana Wanda suke cewa.

Sababbin Hotunan Shugaba Muhammad Buhari Da Matarsa Aisha Buhari Cikin Nuna Soyayya

Tuni Dai Akayi Jana’izzar Marigayin A Gidan Sa Dake Rugar Bayero A Bayan Kasuwar Yan Lemo A Garin Mararraba /Nyaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button