Sakowar dalibai 30 Cikin 102 da ‘yanbindiga suka sace a birnin yauri ta Jihar kebbi yasa rundinar sojojin sun.
Sakowar dalibai 30 Cikin 102 da 'yanbindiga suka sace a birnin yauri ta Jihar kebbi yasa rundinar sojojin sun.

‘Yan bindiga sun sako 30 daga cikin ɗaliban sakandaren Birnin Yauri ta Jihar Kebbi da suka sace kusan wata huɗu a arewa maso yammacin Najeriya.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da sakin ɗaliban cikin wata sanarwa da mai bai wa Gwamna Atiku Bagudu shawara kan kafofin yaɗa labarai ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce tuni ɗaliban suka isa gidan gwamnati.
Yahaya Sarki wanda bai bayyana ko an biya kuɗin fansa ba kafin sakin nasu, ya ƙara da cewa “har yanzu ana ƙoƙarin ceto sauran ɗaliban”.
A watan Yunin da ya gabata ne ‘yan bindigar da ake wa laƙabi da ‘yan fashin daji suka afka harabar makarantar ta Federal Government College, Birnin Yauri kuma suka yi awon gaba da ɗaliban da ake kyautata zaton sun kai 102.
Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kuɓutar da wasu daga cikinsu ‘yan awanni bayan sace su.
Kazalika, wasu biyu sun kuɓuta daga hannun ‘yan fashin inda aka tsince su a Jihar Zamfara mai maƙotaka.
To jama’a zamuso mukarbi ra’ayoyinku akan aukuwar wannan lamarin na daliban borin gwari da aka sakesu ajiya zaku iya kasancewa damu a sahinmu na tsokaci.
KU KARANTA WANNAN:
Bayan Zargin Asirin Da Akayiwa Maryam Yahaya Yanzu Wani Bidiyo Ya Bulla Nata
Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.
One Comment