Yadda Fasto Yahunna Buru ya jagoranci kiristoci zuwa taya musulmai murnar maulidi a Kaduna
Yadda Fasto Yahunna Buru ya jagoranci kiristoci zuwa taya musulmai murnar maulidi a Kaduna

Fasto Yohanna Buru wanda shugaban babban cocin Christ Evangelical Intercessory Fellowship ne dake sabon tasha, ya jagoranci kungiyar kiristoci zuwa filin wasa na Ranchers dake jihar Kaduna domin taya Musulmai murnar Maulid, wanda aka gudanar a ranar talata 19 ga watan Oktoba 2021.
Fasto Yahunna Buru ya bayyana cewa, ya kai ziyara filin wasan ne domin taya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyan halitta, Annabi Muhammad (S.A.W). Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kamar yadda jaridar Labaranhausa ta ruwaito cewa, wannan taron da aka yi na maulidi tsakanin addinai biyu, anyi shi ne domin kara dankon zumunci tsakanin al’umma da kuma zaman tare.
A cewar Fasto Yahunna Buru: Annabi na kowa ne ba tare da la’akari da yare, al’ada, launin fata, kasa ko nashiya ba, sabida yayi wa’azi domin a zauna lafiya har zuwa karshen rayuwar shi.
Faston ya kara da cewa: a matsayin sa na jakadan zaman lafiya kuma shugaban kiristoci, zuwan sa wajan musulmai bai sanja masa addini daga kiristoci zuwa musulinci ba.
Faston Yahunna ya kara da cewa: A lokacin kirsimeti musulmai daga yankuna da yawa na Arewacin Nageriya sun saba zuwa su gudanar da taron kirsimeti da kiristoci, a kokarin da suke na ganin sun samar da kyakkyawar alaka a tsakanin mu.
Sannan kuma Faston ya roki dukkan addinai biyun da suyi amfani da wannan lokacin su fadakar dangane da kaunar juna, hadin kai da kuma zaman lafiya a Nageriya baki daya.
Ya kara yin kira ga dukkan musulmai da suyi amfani da wannan lokaci na maulidi wajan yin addu’a kan Allah ya kawo karshen wannan tashin hankali da ake fama da shi a Nageriya.
Ya kara da cewa: Tilas mudinga tunawa da cewa duka mun fito daga tsatso daya ne wato Annabi Adam a Hauwa’u, mu ‘yan uwa ne da kowannen mu ya yarda da littafin sa na qur’ani da Bible, kuma duka mun yarda da mutuwa da ranar tsayuwa sabida dole mu kula da junan mu.
Karanta wannan labarin.
Bayan Zargin Asirin Da Akayiwa Maryam Yahaya Yanzu Wani Bidiyo Ya Bulla Nata
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.