Na Sayar Da Diyata N150,000 Ne Don In Biya Kudin Haya A Cewar Wata Mahaifiya
Na Sayar Da Diyata N150,000 Ne Don In Biya Kudin Haya A Cewar Wata Mahaifiya

Yan Sanda Sun Damke Matar Da Ta Aikata Laifin Sayar Da Yar Cikinta Kamar Yadda Matar Ta Bayyana Cewa Talauchine Ya Ingazata Ta Aikata Wannan Laifin Daga Baya Kuma Tayi Nadama
Jam’in Hukuma Sun Damke Matar Mai Suna Miss Mercy Okon Da Ta Sayar Da Da Diyarta Mai Wata Uku Da Haihuwa A Farashin N150,000 Saboda Rashin Kudi
Mercy Wacce Uwa Ce Mai Yaya Uku Ta Bayyana Cewa Talauchi Ne Ya Ingizata Ta Sayar Da Jaririyarta Saboda Tana Bukatan Biyan Kudi Hayan Gidan Da Take Zaune
Mercy Ta Bayyana Hakan Ne Yayin Tattaunawarta Da Gidan Jaridar Vanguard
A Cewar Mahaifin Jaririyar Ya Rabu Da Ita Lokacin Cikin Na Wata Shida Kuma Bata Da Mai Taimaka Mata
Kamar Yadda Ta Bayyana Cewa ‘Ban Taba Yin Haka Ba ,Na Sayar Da Diyata Ne N150,000 Don Na Biya Kudin Haya Da Kuma Biyan Wasu Bukatun ,Mahaifin Diyar Yayi Watsi Damu Cikin Wata Shida,Bani Da Wani Abu Kuma Abubuwa Sun Yi Tsanani ,Shiyasa Na Bayar Da Diyata Amma Wanda Ya Hadani Da Masu Sayan Jaririan Yace Min Dan Uwansa Na Son Aurena’
Ta Kara Da Cewa Daga Nan Aka Bani N150,000 Kuma Na Karba….Daga Yan Sanda Suka Shiga Lamarin Kuma Aka Kamani.
Ku Kara Karanta Wannan Labarin
Innalillahi An Kashe Shi Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Wurin Zagayen Maulid A Garin Mararraba/Nyaya
Ashe wannan dalilin ne yasa ake zagin mutanen da suke gudanar da maulidi idan shekara ta zagayo
Shi Masu Sauraro Miyai Ra’ayoyinku Game Da Wannan Lamarin.