Ya kamata iyaye su soke kayan lefe da kayan daki domin a sami saukin auratayya, cewar Fauziyya D Sulaiman
Ya kamata iyaye su soke kayan lefe da kayan daki domin a sami saukin auratayya, cewar Fauziyya D Sulaiman

Shahararriyar marubuciya mai suna Fauziyya D Sulaiman wacce ta kasance shugaba wajan taimakawa gajiyayyu ta Creative helping needy faundation, ta bayyana korafinta kan cewa a some lefe da kayan daki inda ta kawo dalilin da dama, wanda dama wasu iyayen basu iya yiwa ‘yayan su kayan daki.
Sai dai an sami korafe korafen jama’a bayan ta wallafa wani koari akan wani murum daya kamar yadda zakuga korafin data wallafa.
Sharhin wani mutum kowa naka yana mai cewa: Malama Fauziyya wallahi ku iyaye mata kune matsalar aure a yanzu, sabida kunfi karfin maza da yawa a cikin sha’anin auratayya a yanzu, ma’ana sau tari zakiga matsalar daga wajan mata take bullowa, ya kamata ki yiwa mata nasiha akan rawar da suke takawa a harkar auratayyar ‘yayan su.
Ki kalli misalin shirin ku na Dadin kowa a wajan auran nuhu kansila wannan ya ishi mai hankali misali, kuma hanyar warware wannan matsalar ita ce, mu koma zuwa ga Allah kawai namiji yafito yana son yarinya mafi yawan mahaifi bai isa ya taka rawar azo a gani ba sabida yadda iyaye mata suke mayar da aure da sha’anin sa, matukar ana so a sami gyaran da kike so a sami to sai uwa ta yarda cewa uban yarinya shi yake da iko ya aurar da ‘yarsa dari bisa dari, a barshi ya taka rawarshi a matsayin sa na maigida.
Amma mafi yawan matayenmu na yanzu sun raina mazajensu musamman a cikin al’umma ta hausawa, ni da ace zan baki wata sharawa da sai ki kirkiri wata na wayar da kan al’umma game da wannan matsalar, mu kuma a haka ne zamu shigo cikkn shirin dan dada wayar da kan al’umma, Allah yasa kin fashimci inda na dosa Ameen.
Amma sai Fauziyya D Sulaiman ta mayar masa da martani kamar haka.
Kowa Naka Kowa Naka idan kaga an raina namiji ka bincika da kyau shi ya fara raina kan sa ta hanyar kasa sauke nauyin dake kan sa, namijin dake kokari akan iyalinsa basu isa yace su sauya ba.
Kalli bidiyon nan domin kaji cikekken bayani.
Karanta wannan labarin.
Mata Guda Bakwai (7) A Duniya Da Bidiyon Tsirachinsu Ya Fita Wadanda Aka Sansu
Karanta wannan labarin.
Yakamata A Daina Yiwa Amarya Lefe Da Kayan Daki Cewar Fauziyya D Suleiman
Karanta wannan labarin.
Na Sayar Da Diyata N150,000 Ne Don In Biya Kudin Haya A Cewar Wata Mahaifiya