Yadda wani matashi mai suna Hamza ya jagoranci masu garkuwa da mutane suka sace mahaifinsa sabida za’a biya shi naira 200,000

Yadda wani matashi mai suna Hamza ya jagoranci masu garkuwa da mutane suka sace mahaifinsa sabida za'a biya shi naira 200,000

Wani matashi mai suna hamza isa dan shekara ashirin da biyar 25 wanda yake zaune a kauyen Ringin Gora, a karamar hukumar matazu dake jihar Katsina ya bayyana cewa ya taimakawa ‘yan garkuwa da mutane wajan sace mahaifinsa daga gidansu domin a bashi la’adar naira budu dari biyu 200,000.

Matashin wanda ake zargin nasa mai suna hamza isah suna samin sabani da mahaifin nasa Alhaji isah maigora wanda yake da shekaru sittin 60 a duniya, Hamza yace ya hada baki da wasu mutane mazauna yaki biyu wanda suma a yanzu haka suna hannun jami’an ‘yan sanda dalilin sace mahaifin sa wanda har yanzu yana hannun masu garkuwa da mutane.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, sufeto Isah Gambo ya gabatar da mutumin da ake zargin tare da sauran wadanda ake zargin, inda aka tare su a gaban manema labarai na rundunar ‘yan sandan jihar a ranar juma’a.

Hamza isah yace: ina da matsala da mahaifina shi yasa naje wajan Auwal magaji domin ya taimakamin da daki kuma yayi alkawarin zai taimakamini, bama daki kawai ba har kudade masu yawa idan zan iya taimaka musu wajan sace mahaifina.

Nan take ya bani dubu ashirin 20,000 sannan kuma yace zai karamin da dubu dari biyu 200,000, a lokacin da aka saxe mahaifina kuma aka biya kudin fansa.

Sai na fada musu cewa, zai yi wahala a sace mahaifina sabida ginin gidanmu yana da matukar karfi, amma sai suka fadamin cewa kada na damu sannan kuma kuma bai layu daban-daban guda shida domin na binne su a gidan namu, daga wannan lokacin ba’a fi kwana uku ba suka shiga gidanmu suka sace mahaifina.

Hamza ya kara da cewa: Nayi kokarin tona asiri bayan anyi garkuwa da mahaifina naje wajan Auwal magaji na sanar da shi cewa, ina so na mayar da kudaden da aka bani amma sai ya yimin barazana da cewa rayuwata zata shiga hadari idan na sake na fadawa kowa, a duk lokacin da suka banu umarni ina shan wahala na yanke shawarar bayyana komai.

A cewar SP Gambo: Babban yayan wanda ake zargin, Buhari Isah, ya fara shakka da kalaman dan uwansa bayan anyi garkuwa da mahaifin su, inda ya bayyana cewa kanin nasa Hamza yana yawan alfahari da cewa nan bada jimawa ba sai sami kudade masu yawa.

Hakan yasa yakira ‘yan sanda domin su binciki al’amarin sannan kuma yayin da ake gudanar da binciken, wanda ake zargin ya bayyana cewa shine ya kitsa cewa a sace mahaifin bayan wani tsaho daga unguwar ya rudeshi da kyautar naira dubu ashirin 20,000, sannan kuma ya masa alkawarin cewa zai biya shi lada mai yawa idan akayi nasara a aikin.

Ga bidiyon nan sai ku kalla domin kuji cikekken bayani akan wannan lamarin.

Karanta wannan labarin.

Rabi’u Rikadawa Ya Bayyana Dalilinsa Na Rungumar Wata Jaruma A Kannywood

Karanta wannan labarin.

Ya kamata iyaye su soke kayan lefe da kayan daki domin a sami saukin auratayya, cewar Fauziyya D Sulaiman

Karanta wannan labarin.

Mata Guda Bakwai (7) A Duniya Da Bidiyon Tsirachinsu Ya Fita Wadanda Aka Sansu

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button