Trending

Yakamata A Daina Yiwa Amarya Lefe Da Kayan Daki Cewar Fauziyya D Suleiman

Yakamata A Daina Yiwa Amarya Lefe Da Kayan Daki Cewar Fauziyya D Suleiman

A Wata Doguwar Bidiyo Da Fauziyya D Suleiman Ta Wallafa A shafinta Na Instagram, Ta Bayyana Cikim Bidiyon Yadda Take Bayar Da Shawara Fa Iyaye A Yanzu Dasu Soke Lefe Da Kayan Daki.

Acikin Bidiyon Da Wakilinmu Ya Kalla A Tsanake Fauziyya D Suleiman Ta Bayyana Yadda Ake Shan Wahala A Yanzu Waje Yin Wadannan Abubuwa Wanda A Al’adarmu Ta Hausa Fulani Ya Zama Dole Sai Munyi.

Sannan Taci Gaba Da Cewa Hakan Yakan Iya Kawo Talauchi Sosai Duba Da Yadda Yam Mata Suka Dauki Karya Suka Dorawa Kansu, Kowacce So Take A Yi Mata Kayan Dasuka Wuce Tunanin Na ‘Yar Uwarta Ko Abokiyarta.

Duk Dai Acikin Bayanin Fauziyya D Suleiman Take Cewa, Yanxu Sai Ka Samu Gida Da Yam Mata Sunfi Biyar Kuma Gidan Sunada Karamin Karfi, Ma’ana Iyayen D Zasuyi Dawainiya Ta Kayan Aure Basu Da Halinyi Sannan Kuma ‘Yan Uwa Kowa Yana Ta Kansa.

Wanda Kuma Sai Kaga Batun Aure Ya Tashi Na Yam Mata Biyu Ko Uku A Lokaci Guda, Wanda Kuma Hakan Yakan Iya Kawo Matsala Ta Shiga Halin Kunchi Da Talauchi Ga Iyaye.

Sai Kaga Anyi Auren Mace Amma Kuma Gidansu Yarinyar Da Akayi Auren Sai Agansu Cikin Wahala, To Ya Kamata A Soke Yin Wadannan Abubuwa Tunda Dama Ba Addini Ne Yace Dole Sai Anyiwa Mace Kayan Daki Ko Kayan Lefe Ba, Addini Abunda Ya Sani Ga Aure Shine Sadaki Da Shaidu Kawai Idan Aka Samu Wadanann Shikenan Aure Yayiwu Sauran Abubuwa Kuma Wannan Al’adarmu Ce Ta Malam Bahaushe.

Zamu Nuna Muku Bidiyon Dai Sai Ku Kalla Domin Kuji Cikakken Bayani Daga Bakinta.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Daya Faru Ko Kuma Shawara Da Fauziyya D Suleiman Ta Fadawa Iyayen Yara A Yanzu Akan Kayan Lefe.

Sannan Zamu So Ku Watsa Labarin Nan Domin Wasu Su San Halin Da Ake Ciki Akan Wannan Shawara Data Bayar, Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Na Sayar Da Diyata N150,000 Ne Don In Biya Kudin Haya A Cewar Wata Mahaifiya

Ku Karanta Wannan Labarin:

Innalillahi An Kashe Shi Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Wurin Zagayen Maulid A Garin Mararraba/Nyaya

Ku Karanta Wannan Labarin:

Sababbin Hotunan Shugaba Muhammad Buhari Da Matarsa Aisha Buhari Cikin Nuna Soyayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button