Labari Mai Dadi Buhari Zai Bawa Masu Digiri Bashin Milliyan Saboda Rage Zaman Banza
Labari Mai Dadi Buhari Zai Bawa Masu Digiri Bashin Milliyan Saboda Rage Zaman Banza

Kamar Yadda Muka Sami Labari Daga Shafin Hausalegit Sun Bayyana Cewa Gwamnatin Tarayya Tace Daliban Da Suka Kammala Karatun Digiri A Nijeriya Zasu Iya Samun Lamuni Har Naira Miliyan Biyar Domin Yaki Da Rashin Aikin Yi
A Cewar Babban Bankin Nijeriya Wasu Na Iya Samun Kusan Miliyan N25 A Ayukan Hadin Gwiwa Da Ayyukan Kamfanin Inda Gwamnatin Tace Wannan Shirin Na Nufin Samar Da Wani Sabon Tsarin Kudin Wanda Zai Bunkasa Samar da Ayyukan Yi
Babban Banki Ya Sanar Da Sabon Shirin Ga Wadanda Suka Kammala Karatun Jami’a Da Kwalejojin Fasaha Dake Son Kafa Kasuwanci Yana Mai Cewa Matakin Wani Bangaren Ne A Kokarinsa Na Yaki Da Rashin Aikin Yi A Kasar
Banki Yace Za’a Aiwatar Da Shirin Lamuni Ne Karkashin Shirin Sa Na Tertiary Institution Enterpreneurship Scheme (Ties)
A Wata Sanarwa Da Babban Bankin Ya Fitar A Shafinsu Na Facebook Yace
‘Babban Banki Na Cbn A Matsayin Wani Bangare Na Manufofin Sa Na Magance Haihuwar Rashin Aikin Yi Ga Matasa Da Zaman Banza,Ya Bullo Da Tertiary Institution Entepreneurship Scheme (TIES) Don Samar Da Canji Mai Kyau Tsakanin Daliban Da Suka Kammala Karatun Digiri Na Kwalejojin Kimiyya Da Jami’o’i A Nijeriya Daga Neman Ayyukan Gwamnati Zuwa Kasuwa.
Wannan Tsarin Na Nufi Baka Bashi Domin Habaka Kasuwancinka Ba Tare Da Ka Kammala Karatu Kuma Kana Ta Neman Aiki Baka Samu Ba Muna Fatan Wannan Kudirin Da Gwamnati Take Niyyar Yi Ya Zamo Alkairi Ga Daliban Da Suka Kammala Karatu Sannan Kuma Suna Zama Banza
Ku Kara Karanta Wannan Labarin
Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Mu Na Tsokaci Game Da Wannan Al’amarin.