yan fashin daji sun yi ajalin mutum 339 a jihohin Zamfara da Kano da Kaduna da Neja cikin watan na Satumba Wanda Hakan Yasa.

yan fashin daji sun yi ajalin mutum 339 a jihohin Zamfara da Kano da Kaduna da Neja cikin watan na Satumba Wanda Hakan Yasa.

Fararen hula kusan 500 ne aka kashe sakamakon hare-hare da tashin hankali daban-daban a faɗin Najeriya cikin watan da ya gabata na Satumba, a cewar wani rahoto.

Rahoton wanda cibiyar West Africa Network for Peace Building (WANEP) ta wallafa kuma ta ruwaito, ya ce jumillar ‘yan Najeriya 944 ne suka mutu kuma 496 daga cikinsu farar hula ne.

Daga cikin kashe-kashen, ‘yan fashin daji sun yi ajalin mutum 339 a jihohin Zamfara da Kano da Kaduna da Neja cikin watan na Satumba kaɗai, a cewar rahoton.

An samu rahotannin kashe-kashe a dukkan ɓangarorin siyasar Najeriya shida.

Yankin arewa maso yamma mai fama da hare-haren ‘yan fashin daji ne kan gaba a yawan waɗanda aka kashe da mutum 193.

An kashe 84 a Kaduna, 4 a Kano, 5 a Katsina, 5 a Kebbi, 70 a Sokoto da Zamfara 25

A cewar rahoton har wa yau, an kashe 13 a Jihar Yobe, 12 a Borno, 7 a Adamawa da kuma 4 a Bauchi, dukkansu a arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram.

A kudu maso gabas kuwa, an kashe 30 a Jihar Anambra, 16 a Imo, 5 a Ebonyi, sai kuma 3 a Enugu.

A yankin kudu maso kudu ma an kashe 30 a Jihar Delta, 4 a Bayelsa, 1 a Akwa Ibom, 2 a Rivers, 3 a Edo.

A ɓangaren kudu maso yamma kuma, mutum 8 ne suka mutu a Jihar Legas, 3 a Ogun, 3 a Osun, 2 a Ondo da kuma 1 da ya mutu a Oyo.

To jama’a zamuso mukarbi ra’ayoyinku akan aukuwar wannan lamarin na kashe kashen da muke Dana dasu a wannan yankin na arewa.

KU KARANTA WANNAN:

Labari Mai Dadi Buhari Zai Bawa Masu Digiri Bashin Milliyan Saboda Rage Zaman Banza

Kalli bidiyon matashin da yayi ikirarin cewa zai sayar naira Miliyan ashirin 20M dalilin baiga Naziru Sarkin Waka ba

Yadda Al’ummar Unguwar Dakata Suka Kuka Kan Bude Gidan Sharholiya Da Ake Kukarin Yi A Unguwar

Subahanallahi An Yankewa Wata Jarumar Kannywood Kafa Saboda Rashin Lafiya

Kada kumanta ku Danna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button