Trending

Idan Nayi Aure Na Haihu Allah Yasa Kada ‘Ya’Yan Dana Haifa Su Zama Jarumin Kannywood Cewar Ummi Zeze

Idan Nayi Aure Na Haihu Allah Yasa Kada Dan Dana Haifa Ya Zama Jaruman Kannywood Cewar Ummi Zeze

Fitacciyar Jarumar Film Fin Hausa A Shekarun Dasuka Shude Ummi Zeze Tayi Wata Addu’a Wanda Ta Zamto Abun Cece-kuce.

Kamar Yadda Kuka Sani A Yanzu Masana’antar Kannywood Tana Wani Bangare Wanda Idan Akaga Mutum Daga Cikinta Anayi Masa Kallo Biyu, Walau Na Kirki Ko Kuma Mutumin Banza Duba Da Irin Badakala Ko Kuma Abubuwan Dasuke Faruwa Marasa Dadi Wanda Hakan Yana Janyowa Masana’antar Bakin Jini.

To Sai Dai Hausawa Sunce Kyawun Dan Kwarai Ya Gaji Ubansa, Yadda Zakaga Mafiya Yawan Mutane Suna Daukowa ‘Ya’Yansu Suna Dorasu A Wajen Harkokinsu Na Kasuwanchi Ko Wani Waje Dasuke Samun Kudi.

Domin Kamar Yadda Wannan Sana’a Ta Rufawa Mahaifin Asiri, Yana Zaton Shina Yaron Daya Haifa Hakan Zata Faru Akansa.

Jaruma Ummi Zeze Tayi Wani Batu Wanda Yaso Ya Janyo Cece-kuce A Kafafen Sada Zumunta, Jarumar Wanda A Kwanakin Baya Ta Tayar Da Wata Kura Har Yasa ‘Yan Jarida Sukayi Hira Da Ita Domin Tabbatar Da Abunda Ta Fada.

Ga Mutanen Dasuka San Abun A kwanakin Baya, Jarumar Ta Taba Ikrarin Kashe Kanta Sakamakon Asarar Wasu Makudan Kudade Da Tayi A Cewar Ta.

Bayan Wannan Kura Ta Lafa Sai Kuma Muka Samu Wannan Gajeren Bayani Da Jarumar Tayi, Dafarko Dai Jarumar Ta Wallafa Hoton Tare Dayin Wani Dan Gajeren Bayani Da Harshen Turanchi Kamar Haka;

ummizeezee Ya Allah here is my prayer ,when ever
you get me “MARRIED “and blessed me with children
do not make them “FILM ACTORS “

Abunda Jarumar Take nufi Shine, Ya Allah Wannan Itace Addu’a Ta, Duk Lokacin Da Nayi Aure Kuma Na Haihu Kada Allah Yasa ‘Ya’Yan Dana Haifa Su Zama Jaruman Kannywood!

Wannan Magana Da Jarumar Tayi Shine Wanda Bahaushe Yake Cewa Barin Zance Domin Mutane Da Dama Sun Tambayeta Ba’asi Akan Haka Duba Da Ansan Harkar Film Itace Sana’arta Kuma ita Ta Rufa Mata Asiri Amma Take Fadin Haka.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinmu A Sashemu Na Tsokaci Akan Wannan Kalami Na Ummi Zeze Akan Harkar Film, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Yin lalata da wasu dalibai Mata a federal college dake bauchi yajawo hukumar makarantar takori malaman da aka samu da laifin a makarantar Wanda Hakan Yasa.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Labari Mai Dadi Buhari Zai Bawa Masu Digiri Bashin Milliyan Saboda Rage Zaman Banza

Ku Karanta Wannan Labarin:

Yadda wani matashi mai suna Hamza ya jagoranci masu garkuwa da mutane suka sace mahaifinsa sabida za’a biya shi naira 200,000

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button