Yabon Annabi s.a.w da jarumar shirin Dadin Kowa Stephanie tayi ya janyo maya cece-kuce a abin fada

Yabon Annabi s.a.w da jarumar shirin Dadin Kowa Stephanie tayi ya janyo maya cece-kuce a abin fada

A karo na biyu jarumar shirin Dadin Kowa Stephnie na kara samin yabo da fatan alkairi daga wajan musulmai bisa ga yadda take nuna soyayyarta ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad (S.A.W), a wannan mata na daulidi watan da daukacin musulmai suke murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyan halitta S.A.W.

A kwanakin baya jaruma Stephanie tabi wakar larabawa wanda ake yiwa Annabi sanati inda ta kwaikwayi yadda ake wakeb a dandalin TikTok wanda hakan yasa aka dinga yabon ta, to a wannan karon ma ta sake rera wakar yabon Annabi da bakinta inda a wannan karon yafi kawatar da mutane inda aka rinka yadawa ana rubuce rubuce na fatan musulinta ga jaruma Stephanie.

Muhammad Salis Hussain ya rubuta  cewa: Kirista ‘yar wasan kwaikwayo Sara Aloysius wanda ake kira da Stephanie ta cikin shirin Dadin Kowa wanda ake nunawa a Arewa24.

Tana rera waken yabon Annabi Muhammad S.A.W, cikin sayyayar murya da biyayya da nuna soyayya ga Annabi S.A.W. sabida samuwarsa cikin wannan wata mai girma.

Abin da yabada mamaki sosai ga sauran al’umma cewa kirita da sallama da yabo ga Annai S.A.W, Allah ya mata rabon shiriya zuwa ga addinin islam.

Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan yabon Annabi S.A.W da jaruma Stephanie tayi ga fiyayyan halitta S.A.W, inda al’umma suke tunanin ko jarumar tana da ra’ayin musulinta ne zuwa nan gaba.

Ba wannan ne karo na farko da jarumar ta fara kwaikwayon waken yabon Annabi s.a.w ba, a kwanakin baya ta kwaikwayi irin wannan waken ba yabon fiyayyan halitta s.a.w, inda a wannan watan da muke ciki na zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad s.a.w jarumar har da kanta ta sake rera waken yabon Annabin tsira s.a.w.

Domin kuji yadda jaruma Stephanie take rera waken yabin Annabi Muhammad s.a.w, sai ku kalli bidiyon dake kasa a, cikin bidiyon zakuga yadda jarumar ta nutsu sannan ta maida hankalinta wajan rera wannan wakar ta yabon fiyayyan halitta Annabi s.a.w.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Karanta wannan labarin.

Haduwar Facebook Ta Jefa Wata Karuwa Acikin Kurkuku, Bayan Daukan Bidiyon Wanda Sukayi Lalata Dashi

Karanta wannan labarin.

Mun Kirkiri Hanyar Dazaka Auri Kowacce Mace Ta Wayarka Cewar Malam Aminu Daurawa

Karanta wannan labarin.

Idan Nayi Aure Na Haihu Allah Yasa Kada ‘Ya’Yan Dana Haifa Su Zama Jarumin Kannywood Cewar Ummi Zeze

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button