Yadda Wata Mata Yar Africa Ta Zamo Mace Ta Farko Data Haifi Yaya Tara A Lokaci Guda

Yadda Wata Mata Yar Africa Ta Zamo Mace Ta Farko Data Haifi Yaya Tara A Lokaci Guda

Halima Cisse Ta Haifi ‘Ya’ya Tara A Asabitin Ain Borja Clinic A Casablanca Morocco Kamar Yadda Kuka Sani A Watan Mayun Shekarar 2009 Ne Wata Mata Mai Suna Nadya Ta Haifi ‘Ya’ya Takwas Da Har Yanzu Suke Araye

A Halin Yanzu Mahaifiyar Yan Taran Ta Bayyana Cewa ‘Ya’ya Suna Cikin Kunshi Lafiya Bayan Wata Tara Da Haihuwarsu Sannan Zata Koma Gida Wato Mali

Matar Mai Shekara 26 Da Haihuwa Ta Bayyana Hakan Ne Yayin Tattaunawar Da Akayi Da Ita A Asabitin Da Ake Kula Da Lafiyarta Da Jariran Da Ta Haifa

Mijinta Mai Suna Kader Arby Mai Shekara 36 Wanda Yake Aiki A Ma’aikatar Navy Ta Mali Ya Bayyana Cewa Haduwarsa Ta Farko Da Jariran Da Aka Haifa Masa Shine A Ranar 9 Ga Watan Juli A Asabitin Morocco

Inda Aka Sanya Wa ‘Ya’ya Hudu Maza Suna Kamar Haka Mohammed , Bah, El hadji Da Oumar Su Kuma Sauran Mata Biyar Din Aka Sa Musu Suna Kamar Haka Hauwa, Adama, Fatouma, Oumou, Da Khadidia

Kalli Bidiyan Anan

Ku Kara Karanta Wannan Labarin

Bidiyan Dinnar Haihuwar Matasa Dake Kunyar Hada Ido Da Juna Sai Gashi Sun Suntulo Yan Tagwaye Bayan Watan Bakwai

Yabon Annabi s.a.w da jarumar shirin Dadin Kowa Stephanie tayi ya janyo maya cece-kuce a abin fada

Muna Fatan Allah Ya Raya Wayannan Yan Taran Ya Albarkacin Rayuwarsu Ya Kara Kawowa Zuria Muslimai Zuria Na Garin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button