Manyan Malamai sun kara kirkiro wani saban al’amari akan Maulidin da akeyi na haihuwar Fiyayyan halitta S.A.W

Manyan Malamai sun kara kirkiro wani saban al'amari akan Maulidin da akeyi na haihuwar Fiyayyan halitta S.A.W

A takaice dai maulidi ya zamo wani abu wanda baza’a daina cece-kuce a kansa ba sannan kuma baza’a iya daina yinshi ba.

Kamar yadda mafi yawancin malamai suka fadi cewa anhaifi manzon Allah s.a.w a ranar 12 ga wannan watan da muke ciki na Rabiul Auwal, inda bayan kwana 7 da haihuwar sannan kuma itace ranar suna kamar yadda yazo a al’adar malam Bahaushe.

Sai dai shi malam Bahaushe yana da wata al’ada bayan wannan wanda ake yanka wata dabba sannan a dafa namanta ayi romo domin mai jego tasha dadi, kuma Bahaushe yana yin wannan al’ada ne bayan kwana 5 da haihuwa wannan al’ada itace malam Bahaushe yake kira da kauri.

Sannan kuma bayan kwana 7 da haihuwa sai a sake yanka wata dabbar ita kuma sai a soya namanta, shi kuma wannan naman na bayan kwana 7 da haihuwa shi ake kira da naman suna.

To tun lokacin da aka fara maulidi akan yanka dabbobi a ranar 12 ga watan wato ranar haihuwar Manzon Allah s.a.w, sai kuma bayan kwana 7 a sake aiwatar da wata hidimar wato ranar suna wanda ake kiran ranar da Takutaha.

To a halin yanzu dai wasu sun fara yin naman kauri na haihuwar Manzon Allah S.A.W, wato ranar 5 ga watan haihuwar.

Ga bidiyon nan domin kuji cikekken labari.

Karanta wannan labarin.

Kalli Yadda Jarumar Kannywood Take Dambe Da Karamin Yaro Hannatu S Usman

Karanta wannan labarin.

Jaruma Hadiza gabon ta fita kasar waje domin shakatawa bayan rigimar su ta lafa da Auwal Isah west

Karanta wannan labarin.

Dalilin Dayasa Na Daina Soyayya Da Adam a Zango Cewar Nafisat Abdullahi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button