Sako zuwa ga jarumi Adam a zango akan abin daya aikata akan marayun Zariya

Sako zuwa ga jarumi Adam a zango akan abin daya aikata akan marayun Zariya

Malam Bashir Yahuza Malumfashi shi ne Editan Labarai na jaridar Aminiya.

Daga: Fimmagazine

Ba tare da bata lokaci ba na rubuta maka wannan sako ne da nufin jin inda aka kwana dangane da dangane da babban abin alkairin da akayi ka aikata a bara Oktoba 2020, inda aka sanar da al’umma cewa ka fidda zunzurutun kudade kimanin Naira Miliyan arba’in da bakwai 47 domin daukar nauyin wasu yara marayu sama da guda dari 100,  a wata makaranta mai zaman kanta, Professor Ango Abdullahi College.

Babban dalilin da yasa na tado da wannan batun shine, sabida a bara dai-dai wannan lokacin al’amarin naka ya tada kura a kafafan sada zumunta na soshiyal midiya da kuma jarida, Mujallu, Gidan Radio da Talabigin.

A wannan lokacin al’umma da yawa sunyi ta kokwanto akan al’amarin har ma wasu suke mutanen kai tsaye suka karyata, inda wasu ma suka nemi taba mutuncinka.

Idan baka manta ba ni kadai na daga jaridar Aminiya na kira ka a waya sau uku 3 baka daga ba sannan na tura maka tes amma kaki ka amsa tambayarmu, haka muka gaji muka buga labarin ta hanyar abin da muka sami daga hukumar makarantar da kuma wani bangare na fadar mai sarkin zazzau.

Haka kuna bara dai manyan ‘yan jarida na Arewa irin su Malan Ibrashim sheme da Malam Jaafar jaafar duk sunyi kokarin bin diddigin al’amarin ba tare da samin gamsasshen bayani ba.

A yanzu, na tado da bayanin nan ne domin mu ji daga bakin ka, shin me ake ciki game da wannan babban aikin alheri da ka ce ka ɗabbaƙa a bara? Har yanzu ka na ci gaba da ɗaukar nauyin yaran nan kuma wane matakin karatu su ke a yanzu.

Amsoshin da ka bayar za su inganta al’amarin nan kuma ka wanke wa masu kokwanto dukkan shakku. Haka kuma aikin naka zai zama abin koyi daga jaruman fim irin ka, kasancewar duk wanda ya assasa alheri kuma aka yi koyi da shi, zai rabauta ninkin-ba-ninkin.

Karanta wannan labarin.

Bidiyan Yadda Ake Kari Da Dollars Kamar Ruwa A Birthday Din Yar Gidan Mawaki Davido

Karanta wannan labarin.

Rasa Dan jaridar da akayi tsawon sati biyu yadagawa Gwamnati hankali Wanda yasa tafara tunanin tayi.

Karanta wannan labarin.

‘Yan Izala sun fara samin rarrabuwar kai akan masu yin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button