Yanzu Aka Bankado Wani Sirri Akan Adam A Zango Game Da Almajirai
Yanzu Aka Bankado Wani Sirri Akan Adam A Zango Game Da Almajirai

Fitaccen Jarumin Film Din Hausa Ta Kannywood Wato Adam A Zango Ana Zarginsa Da Kin Cika Alkawarin Daya Dauka Akan Almajirai Da Marasa Karfi A Kwanakin Baya, Wanda Yayi Alkawarin Daukan Nauyinsu Amma Yanzu Abun Yayi Shiru.
Kamar Yadda Wani Mutumi Yayi Dogon Tsokaci Akan Shafin Facebook Game Da Adam A Zango Ya Wallafa Wani Dogon Bayani Game Da Al’amarin Ga Yadda Abun Yake.
Wai Ina Aka Kwana Game Da Batun Marayun Da
Adam A. Zango Ya Dauki Nauyin Karatunsu A GarinZaria?Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan ka na lafiya, Allah sanya haka, amin.
Bayan haka, ba tare da bata lokaci ba, na rubuto
maka wannan sako ne da nufin jin inda aka kwana
dangane da babban abin alherin da ka yi ikirarin ka
aikata a bara (Oktoba 2020), inda ka sanar da
al’umma cewa ka fidda zunzurutun kudi, kimaninnaira miliyan 47, domin daukar nauyin karatun wasu
yara marayu sama da 100, a wata makaranta mai
zaman kan ta, mai suna ‘Professor Ango Abdullahi
College’.
Babban dalilin da ya sanya na tado maka da wannan
batu shi ne, saboda a bara, daidai lokacin nan,al’amarin naka ya tada kura a nan kafafen sada
zumunta na soshiyal midiya da kuma jaridu, mujallu,
rediyo da talabijin.
A wancan lokacin, mutane da yawa sun rika tababa
da kokwanto kan al’amarin, har ma wasu kai-tsaye su
ka karyata ka, wasu ma har su ka nemi taba mutuncinka.
ldan ba ka mance ba, ni kai na daga jaridar Aminiya
na kira ka a waya sau uku, ba ka daga ba, kuma na
turo maka tes amma ka ki amsa tambayar mu. Haka
mu ka gaji mu ka buga labarin ta hanyar abin da mu
ka samu daga hukumar makarantar da kuma wani
bangare na fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau.
Haka kuma, a barar dai, manyan yan jarida na Arewa,kamar Malam Ibrahim Sheme da Malam JaafarJaafar, duk sun yi kokarin bin diddigin al’amarin ba
tare da samun gamsasshen bayani ba.A yanzu, na tado da bayanin nan ne domin mu ji daga
bakin ka, shin me ake ciki game da wannan babban
aikin alheri da ka ce ka dabbaka a bara? Har yanzu ka
na ci gaba da daukar nauyin yaran nan kuma wane
matakin karatu su ke a yanzu?
Amsoshin da ka bayar za su inganta al’amarin nankuma ka wanke wa masu kokwanto dukkan shakku.Haka kuma aikin naka zai zama abin koyi dagajaruman fim irin ka, kasancewar duk wanda ya assasa
alheri kuma aka yi koyi da shi, zai rabautaninkin-ba-ninkin.
Ku Saurari Wannan Bidiyon Domin Kuji Cikakken Bayani.
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Batun Karya Alkawari Da Jarumi Adam a Zango Game Da Alkawarin Daya Dauka Akan Almajirai.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Sako zuwa ga jarumi Adam a zango akan abin daya aikata akan marayun Zariya
Ku Karanta Wannan Labarin:
‘Yan Izala sun fara samin rarrabuwar kai akan masu yin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W
Ku Karanta Wannan Labarin: