Yara ‘kanana dubu talatin da shida akasanya a makarantar Wanda sukashafe kwanaki basa Zuwa a Cikin Jihar jigawa yaran sun.

Yara 'kanana dubu talatin da shida akasanya a makarantar Wanda sukashafe kwanaki basa Zuwa a Cikin Jihar jigawa yaran sun.

An sanya Akalla kananan yara dubu talatin da shida a Makarantu bayan sun shafe wasu lokuta basa zuwa makarantu a fadin jihar Jigawa.

Daraktan tabbatar da ingancin aiki na hukumar ilimi a matakin farko ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Iliya shine ya bayyana hakan a lokacin bikin yaye daliban kungiyoyin kare hakkin kananan yara na makarantar firamare da sikandiren kwana ta Kudai wanda kungiyar Save the Children reshen jihar Jigawa ta shirya.

A cewarsa, an samar da cibiyoyin koyar da ilimin manya dari tara da ashirin, inda kuma ake baiwa dalibai mata kayan makaranta kyauta karkashin shirin bada ilimi ga kowa da yake samun tallafi daga bankin duniya.

Ya ce ilimin ‘yaya mata kyauta ne a jihar nan, inda ya bukaci iyayen yara su yi amfani da wannan damar wajen sanya yayansu a makarantu domin cin gajiyar shirin.

A jawabin da ta gabatar, shugabar makarantar kwana ta Kudai, Hajiya Aisha Abubakar ta yaba da kwazon daliban, inda ta bukace su da su kasance jakadun makarantar nagari a makarantun da za su je nan gaba domin ci gaba da neman ilimi.

Ta bukaci daliban su ci gaba da amfani da ilimin da suka samu a kungiyoyin daliban domin fadakar da al’umma.

KU KARANTA WANNAN:

Yanzu Hamisu Breaker Ya Bayyana Wanda Ya Kashe Auren Momi Gombe Sannan Ta Shigo Kannywood

 

Bidiyan Rigimar Teema Makashi Da Musa Mai Sana’a A Gidan Biki Har Tayi Sillar Fadawarsa Cikin Ruwa

 

Hotuna: Wata tsohuwa ‘yar shekara 82 tayi wuff da wani matashin saurayi mai shekara 36 a kasar Ingila

 

Kada Kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button