Rundinar sojojin Nigeria tayi nasarar kashe wasu mayakan Boko Haram Samada mutane 35 daga Ciki harda wani saban Shugaban kungiyar (ISWAP) mai suna malam bako.

Rundinar sojojin Nigeria tayi nasarar kashe wasu mayakan Boko Haram Samada mutane 35 daga Cikin harda wani saban Shugaban kungiyar (ISWAP) maisuna malam bako

Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce ta yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram sama da 38 ciki har da sabon shugaban kungiyar ISWAP wanda ake kira Mallam Bako.

Hukumomin tsaron sun ce sun samu wannan nasara ce a hare-haren da suka rika kaiwa ta sama da ta kasa a cikin mako biyu a karkashin shirin Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabas.

Sojin sun kuma ce hare-haren sun sa mayakan Boko Haram da iyalansu sama da dubu daya sun mika wuya a tsawon wannan lokaci.

A wata hira da akayi da manema labarai Wanda Daya daga Cikin manema labaranmu yasami damar nadomana sautin wani jami’i a sashen hulda da ‘yan jarida na shelkwatar tsaron, Kawamanda AbdulSalam Sani ya ce, sojojin na samun nasara a yankin arewa maso yamma a yaki da barayin daji.

Daga cikin nasarorin, sojojin sun ce sun hallaka barayin daji sama da 70, kuma sama da 50 daga cikinsu a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna ne.

Sauran kuwa a sassan jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kebbi ne, kamar yadda sojojin suka ce.

Sai dai kuma babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na sojojin na Najeriya.

Har yanzu dai akan samu hare-haren da ‘yan Boko Haram ke kaiwa a sassan arewa maso gabashin Najeriyar, yayin da su kuma ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar wasu sassan arewa maso yammacin kasar, duk da nasarar da hukumomin kasar ke cewa suna samu a kansu.

To jama’a zamuso mukarbi ra’ayoyinku akan wannan lamarin na Yan Bindiga zakuma kubiya biyomu kaitsaye ta sahinmu na tsokaci.

A harkulum Kuna tare da Ni  A.Isman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews Dauke da Labaran Duniya .

KU KARANTA WANNAN:

Innalilahi wa Inna ilaihir rajiun ansami hasarin mota da daliban makarantar kwallejin sa’adatu Rimi Wanda mutane biyar 5 suka Rasa ransu.

Bidiyan Manyan Attajirin Kasarna A Makkah Dangote ,Mangal ,Abdulsamad BUA Yayin Ibadah A kasa Mai Tsarki

Mutuwar Jarumar Kannywood Amal Umar Yanzu Gaskiya Ta Bayyana innalillahi

Jaruma Nafisa Abdullahi ta cikin shirin, LABARINA, ta sami daukaka na zama jakadiyar kamfanin Pepsi Naija

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button