Gaskiyar Magana Akan Film Din Batsa Da Jarumar Kannywood Tayi Zainab Indomie
Gaskiyar Magana Akan Film Din Batsa Da Jarumar Kannywood Tayi Zainab Indomie

A Wata Doguwar Hira Da Jarumar Kannywood Tayi Da ‘Yan Jarida Wato Zainab Indomie Ta Bayyana Yadda Rayuwarta Takasance Bayan Shigowarta Harkar Film Da Kuma Halin Da Take Ciki Yanzu.
Bayanin Jarumar Ya Fara Kamar Haka, Da Farko Sunana Zainab Abdullahi Wanda Akafi Sanina Da Zainab Indomie A Harkar Film, Ni ‘Yar Asalin Garin Abuja Ce Kuma Acan Nake Rayuwata Har Yanzu.
Nayi Makarantar Firamare Da Sikandare A Garin Abuja Sannan Sai Nayi Diploma Ta A Jihar Kaduna, Daga Nan Na Shiga Harkar Film Duba Da Tun Ina Karama Nake Sha’awar Kallon Fina-finan Hausa Sosai.
A Duk Lokacin Danake Kallon Film Din Hausa Ina Kasancewa Cikin Jin Dadi Da Kuma Nishadi, Hakanne Yasaka Nake Burin Ana Damawa Dani A Harkar Sai Kuma Gashi Allah Ya Nufa Na Shigo Ciki Kuma Har Na Zama Wata Tauraruwa A Duniyar Fina-finai.
Kafin na shiga harkar fim na yi fadi-tashi sosai, Ina cikin fadi-tashin ne Allah Ya hada ni da Ali Nuhu, bayan na fada wa iyayena sun amince sai suka damka ni a hannunsa a matsayin amana. Daga nan ne ya yarda ya kuma rika sanya ni a cikin fina-finansa.
Ba ni da wani ubangida a harkar fim da ya wuce Ali Nuhu har yau kuma har gobe. Ya ma wuce ubangida ya zama uba kuma dan uwana. Fim din da na fara ko kuma na ce wanda ya haskaka ni shi ne ‘Garinmu Da Zafi’. Wannan fim din shi ne fim din da na fi so duk a cikin fina-finan da na yi.
A Ina Kika Samo Lakabin Zainab Indomie?
Bayan Jin Wannan Tambayar Sai Jarumar Ta Kada Baki Tace, Nasan Kowa Zai So Yaji Yadda Akayi Na Samo Wannan Sunan, To Lokacin Danake Firamare Babu Abinchin Danafiso Sama Da Taliya, Hakane Ya Saka Na Dauki Taliyar indomie A Matsayin Abinchin Danafiso A Rayuwata Har Daga Karshe Ake Tsokanata Da Wannan Sunan Zainab Indomie Tun Banaso Har Ma Ya Zamto inkiya.
Menene Dalilin Ramewarki A Kwanakin Baya?
Jarumar Ta Bayyana Dalilin Rage Kibarta Kamar Haka; A baya idan mutane za su iya tunawa na yi jiki sosai, a gaskiya idan har kana da jiki to za ka sha wahala wurin gudanar da sauran ayyuka musamman ma mu ‘yan fim.
Idan akwai wani rol wanda ya shafi rawa ko gudu ko tsalle-tsalle, to dole idan har kana so ka sake, ka ji dadin jikinka sai idan ba ka da kiba, domin idan kana da kiba bayan an gama za ka ji ka wahala sosai, sannan ba za ka yi rol din yadda ake so ba.
Don haka ba wai jinya ko tashin hankali ko tunani ko yunwa ba ne suka sanya na rame ba, a’a, na rage kiba ne, wanda ake kira ‘slimming’ da Turanci.
Me Zakice Bayan Bullar Hotunanki Wadanda Basu Dace Ba Wanda Zamu Iya Kiransu Da Tsiraichi?
A Gaskiya Ban San Me Zance Ba Kawai Mutane Ne Suke Kirkirar Haka Domin Su Bata Min Suna, Ganin Cewa Na Samu Daukaka A Duniyar Fina-finan Hausa Kuma Yana Sona, Sannan Bana Zama Da Mutane Da Zuciya Daya Kowa ina Kaunarsa Tare Da Girmama Wanda Ya Girmeni Na Mutunta Wanda Na Girmeshi.
Me Yasa Ba’a Ganinki Acikin Fina-finai Kwanan Nan?
Na san mutane za su ce a yanzu an daina yi da ni, to su sani ba haka ba ne. Idan ba za ka manta ba a baya na ce maka na yi difloma a Kaduna, kuma kowa ya sani taura biyu ba za ta taunu ba.
Hakan ya sanya na ajiye harkar fim har sai da na kammala karatuna, amma nan ba dadewa ba masoyana za su fara ganin sababbin fina-finaina.
Zaku Iya Kallon Wannan Bidiyon.
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Ma Tarihin Rayuwar Zainab Indomie Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shire-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Ku Karanta Wannan Labarin:
Yadda Sojoji Suka Hallaka Kasurgumin Dan Arewa Biafra Da Cafke Daya
Ku Karanta Wannan Labarin:
Karamin Yaro Mai Tsantsar Saurin Fahimta Da Ganewa Da Yayi Fice A Duniya