Kaitsaye Bazamukira ‘yanfashin Daji da ‘Yanta ‘adda ba saboda Menene ma a’nar Taddancin?

Kaitsaye Bazamukira 'yanfashin Daji da 'Yanta 'adda ba saboda Menene ma a'nar Taddancin?

  Majalisar dinkin Duniya ta bayyana a kudiri mai lamba 49/60 cewa za a iya fayyace aikin ta’addanci kamar haka.

Wani aiki da aka aikata da nufin saka jama’a cikin tashin hankali, ko kuma wani rukunin mutane ko wasu mutane da manufar siyasa ba tare dawani dalili ba, ko da kuwa mece ce manufarsu a siyasance, ko akida, ko tunani, ko launi, ko kabila, ko addini ko kuma duk wata hanya da za a bi wajen kafa hujjar yin hakan.

A Najeriya, Dokar Ta’addanci ta 2011 ta tanadi hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin aikata ko taimaka wa wanda ya aikata ta’addanci.

Sai dai an yi wa dokar kwaskwarima a 2013 inda aka mayar da hukuncin zuwa daurin ra-da-rai ga wanda ya aikata da kuma hukuncin ɗaurin shekara 20 mafi karanci ga wanda ya taimaka.

Sai dai dokar ba ta fayyace hakikanin ma’anar ta’addanci ba.

Idan ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda gwamnatin Najeriya kan iya kafa kotuna na musamman domin yi wa ‘yan fashin daji shari’a da zummar yanke musu hukunci cikin sauri.

Kazalika, za ta iya matsa wa kasashe makota wajen taso keyar duk wanda ta zarga da shiga ayyukan fashin daji idan ya tsallaka kan iyaka.

Sai dai ba lallai ne ƙasashen su kalle su a matsayin ‘yan ta’adda ba.

To jama’a zamuso mukarbi ra’ayoyinku akan wannan bayanin Nawa na ma’anar Yan ta’adda.

Domin Jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye ta sahinmu na tsokaci A harkulum dai nine naku A.Usman Ahmad Dauke da Labaran Duniya kaitsaye a shafinmu na Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN

Yadda Sojoji Suka Hallaka Kasurgumin Dan Arewa Biafra Da Cafke Daya

Karamin Yaro Mai Tsantsar Saurin Fahimta Da Ganewa Da Yayi Fice A Duniya

Masha Allah: Sulaiman Isah wanda ya auri Baturiya ya wallafa hotunan su tare yana yiwa al’umma barka da juma’a

Bidiyan Bikin Rahma Dantata Da Sheikh Ahmed/Zaman Bautar Kasa Ne Yayi Sillar Aurenmu

Kada Kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button