Advertisement

A cikin kwana 3 kacal mun sami ribar Naira miliyan daya da dubu bari biyu da arba’in da biyar da bari biyar (N1,245,500) a fim din mu mai suna Fanan, inji Mansurah Isah

A cikin kwana 3 kacal mun sami ribar Naira miliyan daya da dubu bari biyu da arba'in da biyar da bari biyar (N1,245,500) a fim din mu mai suna Fanan, inji Mansurah Isah

Kamar yadda dazu muka kawo muku labari akan shirin fim din tsohuwar jarumar masana’antar kannywood mansurah Isah, inda suka haskaka fim din nasu suna Fanan a wata cinima Platinum inda har manya-manyan jaruman kannywood suka halarci wajan.

A yanzu kuma tsohuwar jarumar ta sake wallafa wani sabon labari a shafinta na Instagram akan wannan sabon shirin nata mai suna Fanan, ga labarin kamar haka.

Fim din Fanan ya bude da babbar kasuwa a sabuwar sinimar nan Platinuncenimesng, fim din ya hada naira miliyan daya da dubu dari biyu da arba’in da biyar da dari biyar (N1,245,500), a sinima daya rak a ranar farko (1st Day).

Tabbas fim din Fanan ya dau hazo alabashi a akan yanar gizo duba da yadda wakar fim din mai taken Fanan wanda mawakin zamani Umar M Shareef ya rera ta zama Charbuster Song tun daga satin data fita wanda babu tantama tana daya daga cikin jigon wannan babbar nasara.

Tambaya?

Shin Masu Karatu Kuma Ganin Nan Da Wata Daya Wanne Kudi Film Din Fanan Zai Kawo?

Zamu So Ku Ajiye Mana Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Film Din Wato Fanan.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Noor Buhari Tayi Amai Ta Lashe Kan Halarchin Da Zatayiwa Talakawan Nijeriya Da Suka Nuna Soyayyarsu Ga Mahaifinta

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button