Kalli yadda jaruman kannywood maza da mata suka rakashe a wajan haskaka sabon shirin fim din su mai suna Fanan
Kalli yadda jaruman kannywood maza da mata suka rakashe a wajan haskaka sabon shirin fim din su mai suna Fanan

Kamar yadda kuka sani Mansurah Isah tsohuwar jaruma ce a masana’antar kannywood wanda tayi sharafin ta a shekarun baya wanda har kawo yanzu bata shirin fim.
Mansurah Isah ta kasan ce mata ga ficaccan jarumin kannywood kuma mawaki Sani Musa Danja, wanda shima yanzu baya fitowa a shirin fina-finan kannywood.
Tsohuwar jaruma Mansurah Isah a wannan lokacin ne suka fara haskaka sabon shirin su a wata sabuwar cinima mai suna, Platinum, wanda sunan shirin nasu Fanan.
Kamar yadda wasu suka fara jin sunan fim din a cikin wata sabuwar waka wanda shahararran mawaki, Umar M Shaeef ya rera ta.
Da yawa daga cikin manya-manyan jaruman kannywood sun sami damar halartar wajan haskaka wannan sabon fim din mai suna Fanan, kamar yadda zaku ga jaruman a cikin bidiyo da hotunan dake kasa.
A cikin cinimar da aka haskaka wannan sabon fim din, zaku yadda jaruman suke cashewa da rakashewa a cikin cinimar suna nuna farin cikin su ga haskaka sabin fim din.
Asalin bidiyon mun samo tane daga tashar Youtune mai suna Tsakar gida, wanda tashar ta tattara bidiyo tare da hotunan jaruman da suka halarci wajan haskaka sabon fim din mai suna Fanan.
Jaruman da suka halarci wajan haskaka sabon shirin fim din sun hada da, Sani Musa Danja, Ali nuhu, tare da wasu jarumai mata a kannywood din.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.
Karanta wannan labarin.
Bayan Rashin Lafiyar Maryam Yahaya Yanzu Wani Bidiyonta Ya Sake Bulla Mai Ban Mamaki
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
Jerin Sunayen Sabin Zababbun Shugabannin Jam’iyyar PDP Na Kasa