Trending

Abunda Zai Hana Mace Shiga Aljannah Ko Tana Sallah Idan Har Ta Mutu Tanayi

Abunda Zai Hana Mace Shiga Aljannah Ko Tana Sallah Idan Har Ta Mutu Tanayi

A Wani Dogon Jawabi Dauke Da Nasiha Da Jaridar Rariya Ta Wallafa, Wansa Yake Dauke Da Wasu Laifuka Wanda Mata Sukeyi, Kuma Sanadiyyarsa Yakan Iya Hana Mace Shiga Aljannah Idan Har Ta Mutu Tanayi.

Ga Abunda Shafin Suka Wallafa Wanda Yake Zamtowa Izna Ga Mata Masu Aikata Wannnan Laifi Bayaninsu Ya Fara Kamar Haka;

1) Duk Matar da take da aure tayi zina.

2) Duk Matar da ta Mallaki Mijinta ta hanyar asiri ko ta hanyar tsafi.

3) Duk Matar data Hana kishiyarta ta zauna da Mijinta lafiya.

4) Duk matar da ta raba mijinta da ‘ya’yansa,ko ta Hanyar Asiri ko Yaudara.

5) Duk matar data raba mijinta da Yan uwansa ta hanyar asiri ko yaudara.

6) Duk matar da tayi asiri akan saukarwa
kishiyarta jinin haila duk ranar kwananta sai haila tazo mata.

7) Duk matar da tasa aka daure mahaifar
kishiyarta,don kar ta haihu.

8) Duk matar data dauko ciki a waje ta bawa mijinta,kuma ta tabbata ba nasa bane.

9) Duk matar da tayi daurin baka ga mijinta don yayi mata kishiya.
Ma’anar Haka shine: Duk ranar da zai kwana a dakin kishiyarta sai ya zamanto bana miji ba.Amma idan ya dawo
dakin matsafiyar sai ya dawo namiji.

10) Duk matar data nemi mijinta ya saketa, alhali baya cutar da ita.Kuma ba yadda ya iya.

11) Duk matar da bata godewa mijinta bisa ga irin abubuwan da yake mata na Alkhairi.

12) Duk matar da take cutar da mijinta da bakinta.

13) Duk matar da batayin wankan janaba,
bayan ta sadu da mijinta,ko batayin wankan haila ko biki.

14) Duk matar da take tona asirin mijinta a
cikin kawayenta

15) Duk matar da take annamimanci

16) Duk matar da take sa kayan da yake nuna tsiraicinta,irin wanda musulunci yake fada akan irin shigar yahudawa da nasara.

17) Duk matar data kara gashi akan nata.

18) Duk matar da tilastawa mijinta yayi mata wani abu wanda ba zai iya yi ba.

19) Duk matar data dauki dan wani ta bashi Mama (Nono) bada izinin Mijinta ba.

20)Duk matar da zata cewa Mijinta tunda
muke dakai meka taba yi mini.

Dukkan wadannan Laifuka guda 20, ko wani
guda daya a ciki, idan Mata ta mutu tanayi
bazata shiga Aljannah ba, Koda zata shiga sai
an Babbaka ta.

WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH(S.A.W).

Manzon Allah (s.a.w) yace:Waye zai karbi wadannan kalmomi guda 5 daga gareni, yayi amfani da. su koyasanarda wanda zaiyi amfani dasu ???”Sai Abu Huraira (r.a) yace Ni zan karba ya Ma’aikinAllah.

Sai Manzon Allah (s.a.w) yariqe hannu na ya maimaita minsu sai yace,
1. “Ka guji aikata sabo, zaka zamo
wanda yafi kowa bauta a cikin mutane.
2. “Ka yarda da abinda Allah Ya baka, zakafi
kowaarziqi cikin mutane.
3. “Ka kyautatawa maqobcin ka, zaka
zamo (cikakken) Mumini.
4. “Kasowa mutane abinda kake sowa kanka,
zakakasance (cikakken) Musulmi.
5. “Kada ka yawaita dariya, domin yawan
Dariya na
kashe zuciya.

@SILSILATUL AHAADIISUS SAHIHA

930.MANZON ALLAH (S.A.W) YACE KA
RIQESU KOKA SANAR DA WANDA ZAIYIAMFANIDA SU.

IDAN KA TURAWA YAN’UWA MUSULMA
BAKASAN WA ZAI YI AMFANI DA SU BA,KAGA KASAMU LADANMUTANE MASU TARIN YAWA.Allah bamu iKon kiyayewa Ameen.

To Allah Ya Bamu Ikon Kiyayewa Kuma Allah Ya Shiryemu Baki Daya, Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Sheikh Sudais ya samar da mutum-mutumi da zai dinga tsaftacewa da raba ruwan Zam-Zam a Masallacin Manzon Allah

Ku Karanta Wannan Labarin:

Budurwar Data Zagi Malaman Addini Kuma Tace Suna Aikata Zina Yanzu Ta Nemi Gafararsu

Ku Karanta Wannan Labarin:

Bayyanar Hoton Hadiza Gabon Rungume Da Danta Mai Shekara 18 Ya Janyo Cece Kuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button