Sheikh Ahmad Gumi ya soki Gwamnatin shugaba Buhari da cewa kada su ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda
Sheikh Ahmad Gumi ya soki Gwamnatin shugaba Buhari da cewa kada su ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Sheikh Ahmad Gumi ya sake jaddada bukatar sa akan ayiwa ‘yan bindiga afuwa sannan kuma a inganta rayuwar su.
Sheikh Ahmad Gumi ya jima yana gargadin Gwamnatin tarayya akan kada tayi kuskuren bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.
A cewar sa daukar wannan matakin zai sa su hada kai da ‘yan Boko haram da ISWAP, kuma hakan zai jefa ‘yan Arewacin Nageriya cikin mummunan hatsari.
Shahararran malamin addinin musulinci Sheikh Ahmad Gumi ya sake fadar ra’ayin sa akan cewa, yiwa ‘yan bindiga afuwa ne kadai zai sa a kawo karshen zubar da jinin mutane a Arewa.
Sannan kuma ya kara da cewa bayyana ‘yan bindinga a matsayin ‘yan ta’adda zai kara haufar da wasu matsaloli na ta’addanci.
Malam Ahmad Gumi ya fadi wannan maganar ne a wajan sanya marayu rukuni na uku na shirin samar musu da ilimi da kuma kula da lafiyar su kyauta, wanda gidauniyar musulinci dake jihar Kano da dauki nauyin shiryawa.
Sheikh Ahmad Gumi yace: Idan har akwai wata hanya da zata dakatar da zubar da jini zai fi kyau ayi musu kwatankwacin abin da aka yiwa mayakan jiger Delta.
Wanda sun kasance suna fada bututun mai da tare da zubar da jinin mutane, amma a shirye suke da su ajiye makaman su idan har za’a musu afuwa da daukar nauyin su, inaga za’a ayi yiwa ‘yan bindiga haka.
Ya kara da cewa: Mun gana dasu kuma zasu ajiye makaman su amma idan sun dai na kuma ba’a samar musu da ilima ba da kudin da zasu kula da kan su, to zasu koma gidan jiya.
Wannan kadan daga cikin bayanin da Sheikh Ahmad Gumi yayi, wanda yake bukata ayiwa ‘yan bindiga afuwa sannan kuma kada Gwamnati ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.
Karanta wannan labarin.
Budurwar Data Zagi Malaman Addini Kuma Tace Suna Aikata Zina Yanzu Ta Nemi Gafararsu
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
Bayyanar Hoton Hadiza Gabon Rungume Da Danta Mai Shekara 18 Ya Janyo Cece Kuce
2 Comments