Sheikh Sudais ya samar da mutum-mutumi da zai dinga tsaftacewa da raba ruwan Zam-Zam a Masallacin Manzon Allah
Sheikh Sudais ya samar da mutum-mutumi da zai dinga tsaftacewa da raba ruwan Zam-Zam a Masallacin Manzon Allah

Kasar Saudiyya ta kaddamar da wani mutum-mutumi na zamani a Masallacin Harami a ranar Larabar nan da ta gabata, Shugaban kula da al’amuran Masallacin, Sheikh Dr Abdulrahman Bin Abdulaziz Al-Sudais shine ya kaddamar da mutum-mutumin.
An bayyana cewa mutum-mutumin da aka yi da fasahar zamani zai iya daukar ruwa mai yawan lita 68, kuma zai iya shafe awa hudu cur yana aiki, tare da zagaye wuri mai nisan mita 2,000 a kowacce sa’a daya.
Kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito, Dr Al-Sudais ya bayyana cewa, ma’aikatarsa tana kokari wajen aiki da bayyana abubuwan dake wakana wanda Hakan kuma na da nasaba da kokari da yake na gabatar da fasaha a manyan manyan Masallatan biyu da za su yi daidai da zamani.
Hukumar Masallatan ta ce za ta yi kokari wajen tabbatar da cewa duka Mahajjata da masu zuwa Umara sun samu tarbar da ta dace da zarar sun sanya kafar su a cikin Masallatan guda biyu.
Ana fatan ta hanyar samar da kwarewa mafi kyau, aikin hukumar Masallatan zai iya kawo martaba da wayewa ta masarautar wajen hidimar da ake yiwa Masallatan guda biyu masu alfarma ga alhazansu.
Hakazalika, Dr Al-Sudais bai manta da yaba ayyukan na’urorin mutum-mutumi na zamani da aka yi da kuma rawar da suke takawa wajen inganta tsarin hidimar da ake ba wa maziyartan Masallatan bisa sabbin ka’idojin kasa da kasa.
Masarautar kasar Saudiyya dai tabbas tana samun cigaba sosai tare da amfani da fasahar zamani don saukaka ibadar maziyarta da mahajjata da suke zuwa aikin Hajji da Umara, tare da cigaba da bin matakan kariya ga yaduwar annobar COVID-19.
Daya daga cikin amfanin da mutum-mutumin zamanin zai yi wajen inganta ayyukan Masallatan guda biyu dake da ban sha’awa shine, na’urorin za su dinga rabawa Mahajjata ruwan Zamzam inda hakan zai taimaka wajen hana yaduwar annobar cutar COVID-19 a tsakanin alhazai, jaridar Labarunhausa ce ta tattara bayanan.
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
Budurwar Data Zagi Malaman Addini Kuma Tace Suna Aikata Zina Yanzu Ta Nemi Gafararsu
Karanta wannan labarin.
Bayyanar Hoton Hadiza Gabon Rungume Da Danta Mai Shekara 18 Ya Janyo Cece Kuce
One Comment