Subhanillahi Wani Matashi Ya Kashe Kansa Saboda Tsananin Damuwar Da Ta Yi Masa Yawa A Katsina

Subhanillahi Wani Matashi Ya Kashe Kansa Saboda Tsananin Damuwar Da Ta Yi Masa Yawa A Katsina

Wani matashi Ya Kashe Kansa Sabida Tsananin Damuwar Da Tayi Masa Yawa A Katsina, Rahotannin Da Katsina City News Ta Samu Ya Tabbatar Mana Da Mutuwar Yaro Mai Suna Nura Dake Unguwar Tudun ‘Yanlifida A Cikin Garin Katsina Ta Hanyar Rataye Kansa A Saman Rufin Dakin Gidansu

Wata Majiyar Da Ta Nemi A Sakaya Sunanta Ta Sheda Mana Cewa Suna Zargin Matashin Ya Shiga Damuwa Ne Wadda Tayi Dalilin Rataye Kansa , Tun Bayan Da Jami’an Tsaron Yan Sanda Suka Nuna Mahaifiyarsa A Wani Faifan Bidiyo Inda Ake Zarginta Tana Sayen Man Fetur Tana Saidawa Masu Garkuwa Da Mutanen Daji

Koda Yake Wani Dan Uwa Na Jini Ga Mamacin Ya Shaidawa Wakilin Mu Cewa Yaron Yana Da Lalurar Tabin Hankali

Har Wa Yau Majiyar Katsina City News Ta Sheda Mana Cewa, Mahaifiyar Marigayin Malama Umma Mijinta Ya Mutu Tana Da Marayu A Gabanta Da Take Dawainiya Dasu ,Shine Dalilin Da Yasa Ta Shiga Wannan Sana’a Ta Safarar Man Fetur Zuwa Garin Magamar Jibiya, Amma Sun Sheda Mana ,A Iya Saninsu, Matar Bata Da Alaka Da Masu Garkuwa Da Mutane, Sai Dai Kawai Tana Kai Man Fetur Din Ne Magama, Duba Da Yanda Ake Karancin Fetur Din A Can

Nura Yaro Ne Mai Nutsuwa Wanda Kusan Yana Kula Mun Da Komai Na Kasuwanci Na, Amma Lokacin Da Aka Kama Mahaifiyarsa Ya Shiga Damuwa Har Wata Rana , Yazo Gidan Yace Akwai Wani Da Zai Taimaka Masa Don Mahaifiyarsa Ta Fito , Nace Yayi Hakuri Don Ga Hanyar Da Ake Bi, Muga Abinda Hali Yayi ,Tunda Daga Nan Ya Kama Surutai ,Yace Lallae Sai Na Kasheshi Daga Nan ,Na Fahincin Baya Cikin Hayyacinsa

Ranar Da Zai Rataye Kansa Yana Cikin Shago Sai Naga Ya Tashi Ba Lokacin Da Ya Saba Tashi Ba ,Kuma Har Yana Hawaye ,Sai Na Fahinci Matsalar Da Yake Fama Da Itace Ta Taso ,Shine Nasa Aka Daukeshi Aka Kaishi Gida, Tsakar Dare Aka Cemini Ai Ga Abinda Nura Yayi ‘Inji Dan Uwan Mamacin

Katsina City News Ta Jiyo Mahaifiyar Yaron Data Samu Iskar ‘Yanci Daga Hanun Jami’an Tsaro Tun Gabanin Yaron Ya Kashe Kansa ,Tana Cewa Yaron Ya Shiga Damuwa Ko Bacci Bayayi ,Wani Lokaci Ma Sai Ya Kama Kuka To Amma Dai Muna Rarrashinsa Sai Gami Da Addu’a , Harda Maganguna Saboda Muna Zaton Ko Ya Sami Tabin Hankali

Ranar Da Zai Kashe Kansa Da Daddare Naga Yaki Shiga Daki Ya Kwanta Ya Zauna Waje Yana Kuka Sai Na Lallabaishi Na Bashi Fitila Yaje Daki (Inda Yake Kwana) Ya Kwanta Amma Dukda Hakan Ban Samu Nutsuwa Ba Sai Na Kasa Bacci Na Tashi Na Shiga Dakin Nasa Inga Ya Yake Sai Naga Fitilar Wayar Da Na Bashi Kunne Amma Baya Bisa Shinfidarsa In Duba Sai Naga Yaro Ya Rataye Kansa Anan Ne Nemi Taimakon Jama’a Gami Da Jami’an Tsaro Aka Kaishi Asibiti Aka Tabbatar Mana Da Ya Mutu

Idan Ba’a Manta Ba A Watan Da Ya Shude Ne, Rudunar ‘Yan Sanda Ya Jihar Katsina Ta Nuna Mahaifiyar Yaron A Faifan Bidiyo Tare Da Wasu Mata Biyu Da Ake Zargi Da Keta Doka Ta Hanyar Sayen Fetur Daga Nan Cikin Garin Katsina Zuwa Jibiya

Ku Kara Karanta Wannan Labarin

Ginin Beni Mai Hawa 25 Daya Rushe Dauke Da Mutane Acikinsa A Jihar Lagos

Bayyanar Hoton Hadiza Gabon Rungume Da Danta Mai Shekara 18 Ya Janyo Cece Kuce

Wata karuwa tayiwa matar dadiro dinta duka akan takamasu tare.

 

Daga Karshe Masu Sauraranmu A Koda Yaushe Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Mu Na Tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button