Dama ni musulma ce sallah ce da ibadah kawai banayi, cewar jarumar BBNaija Giftypowers

Dama ni musulma ce sallah ce da ibadah kawai banayi, cewar jarumar BBNaija Giftypowers

Dama ni musulma ce kuma ‘yar kasar Saudia kawai Sallah ce bana yi, cewar jarumar BBNaija Gifty.

Jarumar ta wallafa hotunan ta a shafinta na sada zumunta Instagram tare da fadin wannan magana, inda ta bawa mabiyanta matukar mamaki.

A lokacin da jatumar ta wallafa hotunan ta a shafin nata wanda a ciki hotunan akaga jarumar ta sanya hijabi, wanda hakan ya bawa mabiyan nata mamaki matuka ganin bata saba yin haka ba.

Bayan haka sai jarumar ta bayyanawa mabiyan nata cewa, dama ita musulma ce Sallah ce kawai bata yi.

Sannan tace, ta sayya hijabi ne domin ita ‘yar asalin kasar Saudiyya ce amma ba’a tilasta mata sanya hijabi ba.

Bayan wasu daga cikin mabiyan nata sun mata tsokaci akan sanya hijabin da tayi, sai jarumar ta maida musu da martani kamar yadda zaku gani a kasa.

Sanan kuma zakuga hotunan jarumar mai suna GiftyPowers tare da tsokacin da mabiyan nata suka mata.

Ga hotunan domin ku kalla.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button