Harin da kungiyar ISWAP takai asibitin Malam fatori don ɗiban kayan cikin asibitin sun kashe ƴansanda biyu da sojan Nigeria ɗaya.
Harin da kungiyar ISWAP takai asibitin Malam fatori don ɗiban kayan cikin asibitin sun kashe ƴansanda biyu da sojan Nigeria ɗaya.

Rahotanni daga jihar Borno na cewa ISWAP ta kashe yan sandan Najeriya biyu da soja daya a wani hari da kungiyar ta kai Malan Fatori.
Shafuka da dama sun rawaito cewa jami’an tsaro na daga cikin rundunar hadaka da za su tarbi yan gudun hijira da ake shirin dawowa dasu gida.
A wata mai kama da haka rahotanni daga Magumeri duk dai a jihar Bornon na cewa mahara da ake zaton mayakan ISWAP ne sun kai hari a wani asibiti da ke garin.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito maharan sun buda wuta ne da zuwansu asibitin, sun kuma kona karfen sabis din kamfanin waya na Airtel.
Hakama akwai rahotannin da ke cewa sun kwashi magunguna da sauran kayayyaki.
Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun kasa kansu gida biyu, inda wasu suka rika bata kashi da jami’an tsaro, yayin da daya bangaren ya shiga kwasar kayan asibiti da suka hada da magunguna da firjin da kuma zannuwan gado.
Karamar hukumar Magumeri na da nisan kilomita 40 ne daga birnin Maiduguri na jihar Borno.
Wanda bisa alamu da suka nuna cewa yan ta addan sun yi wannane dama don su kwashi maganin dukan asibiti dakuma sauran kayan aiki baki ɗaya.
To jama’a zamuso mu karbi ta ayoyin akan aukuwar wannan lamari na jihar Maiduguri zaku iya biyomu kaitsaye ta sahinmu na tsokaci.
KU KARANTA WANNAN:
Kada kumanta ku dan mana alamar kararrawar sanar wa domin samun Jin kararrawar sanarwa shirye-shirye masu sauki mungode.