Majalissar wakilai ta dakatar da wani ƙudiri na Halatta Tabar wiwi a kasar Nigeria.
Majalissar wakilai ta dakatar da wani ƙudiri na Halatta Tabar wiwi a kasar Nigeria.

Halat ta tabar wiwi a kasar Nigeriya wannan ba abune da zai iyuba.
Hukumar hana sha da fatauci miyagun kwayoyi tana ɗaukar manyan matakai
Wani kudiri dake kokarin halasta amfani da tabar wiwi domin magani a jiya ya gamu da cikas a majalisar wakilai bayan kwamitin da aka dorawa alhakin tabbatar da ƙudirin ya bayyana adawarsa da ƙudirin.
Shugaban kwamitin kwayoyi na majalisar wakilai, Francis Agbor, yace kwamitin ba zai goyi bayan ƙudirin ba.
Francis Agbor ya sanar da haka a lokacin kare kasafin kudin hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA).
Shugaban hukumar, Buba Marwa, ya bayyana a gaban kwamitin domin kare kasafin kudin hukumar.
Ƴar majalisa Mariam Onuoha ta jam’iyyar APC daga jihar Imo, ita ce ta gabatar da kudirin neman halasta amfani da tabar wiwi domin magani a Najeriya.
Kazalika, shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado Doguwa, na jam’iyyar APC daga jihar Kano, ya gabatar da wani ƙudirin dake bukatar tsaurara hukunci akan ‘yan kasuwa da masu safarar tabar wiwin tare da masu amfani da ita.
Dukkan ƙudirorin suna matakai daban-daban na tabbatar da su.
To jama’a zamuso mukarɓi ra a yinku Alan aukuwar wannan lamari don Jin tabakinku zaku iya biyomu ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Bidiyan Yadda Aka Gudanar Da Birthday Din Maryam Both Tun Bayan Rasuwar Mahaifiyarta
Mutane Biyar 5 sun mutu a yayin wani mum munan hatsari a jihar Kano.
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun damar jin shirye-shirye masu ƙayatarwa mungode.