Yanzu Aka Gano Matsalolin Dasuke Lalata Rayuwar Aure Yanzu
Yanzu Aka Gano Matsalolin Dasuke Lalata Rayuwar Aure Yanzu

A Wani Dogon Bayani Da Shafin Facebook Na Lambun Ma’aurata Ya Wallafa Game Da Matsalolin Da Ake Fuskanta Akan Rayuwar Aurenmu Yanzu, Wanda Hakan Yake Sanadiyyar Lalacewar Zamantakewar.
Acikin Dogon Binciken Da Sukayi Sannan Kuma Da Bayar Da Shawara Game Da Aure Bayanin Nasu Yafara Kamar Haka;
MATSALOLIN DA U KA ADDABIRAYUWAR AURE
1) MATSALAR SHAYE-SHAYEA sannu a hankali dai shan miyagunkwayoyi da zuke-zuken hayaki kala-kala na neman zama ruwan dare tsakanim matasan wannan yanki.
Wannan ya sanya matsalar ta afka har gidajen aure sakamakon daman maaurata na shaye-shayen su tun kafin auren ya riga zame mu su jiki inda ba za su iya rabuwa da shi cikin sauki ba.
Babban abin takaicin ma shi ne yanda
shaye-shayen miyagun kwayoyin kusan ya ke neman komawa ga mata. Yayinda su ka karbe shi ka’in da na’in.
Wasu anhayaudarar ne da cewa ya na kwantar da hankali da kuma kara kyau. Wasu kuma su na sha ne da niyyar yaye damuwa ko kara sha’awa a karshe su buge ta zama yan maye cikakku.
Shari’ar lslama ta zo ne dan kare wasumihimman abubuwa guda biyar na rayuwar dan adam cikin su harda hankalinsa saboda matukar himmancinsa. Idan mutum ya zama ba shi da hankali, to wata dabbar ma ta fi shi domin su dai dabbobi haka nan Allah ya halicce su da daidai hankalin da za su iya
tafi da rayuwar su ta yau da kullum kai
kuwa dan Adam idan ka rasa hankalimusamman sakamakon shaye-shayen
da ka jefa kanka, to tabbas za ka zama
kafi dabba lalacewa.
Yanda shaye-shaye ke shafar zamantakewar aure kuwa shi ne tahanyar damalmala yanayin zaman datashe-tashe hankulan da ba sa ciballantana su cinye.
Shaye-shaye ya kan
sa mutum ya zama mai zargi da saurin
fusata. Wadannan matsaloli kuwa nahaifar da tarzoma a gidajen aure.
Idan magidanta su na shaye-shaye zai
janyo daukewar sha’awa ga mata sannan
kuma ya kawo saurin inzali ga maza.Sannu a hankali sai ka ji rigima ta barke
nan da can.
Hakazalika shaye-shaye ya na haifar damatsalar dukan da fadan dambe agidajen aure. Za ka ga ma’aurata su na
son juna amma kwaya ta sanya za su iya
fita da ga hayyacinsu har su iya ma jibgar
madoyan du cikin halin buguwa.
Wasu a irin wannan halin har su na kaiwada daukar makami su hallaka abinkaunar su da hannun da su ke tarairayar
su a baya.
ldan ana son shawo kan wannan matsala, to dole ne iyaye su zama masu sanya ido da lura da duk wasu sauye- sauyen da su ka gani a wajen yaran su
matasa tun kafin suyi nisa.
Wa su da ga CIkin alamun da iyaye ya kamata suankara da su sun had a da: yawan barci, zama wajen daya ayi shiru bayan matashi bai saba hakan ba, yawan saurin
fushi, kazanta, sauya sabbin abokai
marasa tarbiyya, dauke-dauke, dss.
Da zarar Allah ya sa an lura da wuri to in Allah ya yarda shawo kan matsalar zai zo da sauki, amma idan shaye-shaye ya bi
inin matasa to fa sai dai Allah ne kawaimagani.
Duk matashin da ya ke son daina shaye
shaye kuwa zai iya ta hanyar rabuwa da
miyagun abokan da su ke wannan harkar
tare, da kuma tsarin samun wani abin yi
wanda zai dinga dauke musu kewa, da
kuma yawan anbaton Allah da tsaida
sallah ba wasa da barin wasu ayi wasu a
hankali ita sallar zata hana shi aikata duk
wata alfasha da aikin munkarikamarbyanda Allah ya bada tabbaci a
littafin Sa mai Girma.
Wani malami kuma ya bayyana wata aya
a Suratul-Ma’ida wadda ake rubutawa koa tofa a ruwan zam-zam a baiwa duk
masu shaye-shaye su sha da kyakkyawar niyya idan Allah ya so ya yarda za’a dace.
“INNAMAL KHAUMARU WAL MAISIRUWAL ANSABU WAL AZLAMU RIJSUNMIN AMALISSHAIDAINI
FAJTANIBOOH4″To iya waqafin nan za’a tsaya sai a sake
karantawa ko rubutawa har kafa bakwai7.
Wanda duk baya shan muyagun kwayoyi
ya kiyayi duk wata yaudarar abokai,
kawaye ko samarin da su ka halaka
kuma su ke kokarin hallaka wasu ta
hanyar yaudarar su da karerayen banza
kan miyagun kwayoyi.
Wadanda kuma aka jarrabe su da afkawa wannanmatsalar masu auren da matasan samarida yan matan kuma duk Allah ya dawo mana da su kan hanya madaidaiciya.
Sai kun ji mu a matsala ta gaba wato ta
takwas Mun gode.
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sasheu Na Tsokaci Akan Wannan Shawara Da Suka Bayar Game Da Lalacewar Auratayya, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Ku Karanta Wannan Labarin:
Ku Karanta Wannan Labarin:
An Kama Wani Saurayi Mai Nunawa ‘Yam Mata Al’aurarsa Idan Sun Hadu A Jihar Kano