Yanzu-Yanzu: Rikici ya kaure tsakanin jami’an ‘yan sanda da Direbobin Keke-Napep dalilin bindige wani mai Keke-Napep da dan sanda yayi
Yanzu-Yanzu: Rikici ya kaure tsakanin jami'an 'yan sanda da Direbobin Keke-Napep dalilin bindige wani mai Keke-Napep da dan sanda yayi

Direbobin Keke-Napep sunyi gangami wajan tare hanya sunan fushin su akan kisan da wani dan sanda ya yiwa dayan su a jihar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa: Diribobin Keke-Napep din sun fara wannan zanga-zangar ne bayan wan dan sanda ya kashe daya daga cikin su a bakin titn Meran.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas mai suna, Hakeem Odumosu, ya aika jami’an sintira zuwa yankin da ake wannan zanga-zangar domin samar da zaman lafiya.
Diribobin Keke-Napep din sun tsare ka titin ne da safiyar ranar Alhamis inda suka rufe hanyar shiga da fita dake unguwar Meran, wani yanki dake Abule Egba.
Masu zanga zangar sun dauki wannan matakin ne domin nuna fushin su ga jami’an ‘yan sandan da suke wulakanta su har ma takai ga sun kashe daya daga cikin su.
Wasu na zagin cewa: wani daga cikin jami’an ‘yan sandan ne ya dabawa direban Keke-Napep din wuka lokacin amma wasu suna fadin cewa harbe shi yayi da bindiga, sanan kuma ba yarshi a kan hanya har wa’adin sa ya cika.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa: Rikicin direbobin Keke-Napep da ‘yan sanda ya auku ne akan hanyar Cimmand dake Meran a garin Abula dake Egba a ranar Alhamis.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, shi ne ya tabbatar da faruwar al’amarin ta manhajar Whatapp.
Sannan kuma ya kara da cewa: Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Odusomu, ya tura jami’an ‘yan sanda wajan da ake tarzomar domin samar da zaman lafiya.
Karanta wannan labarin.
Bidiyan Yadda Aka Gudanar Da Birthday Din Maryam Both Tun Bayan Rasuwar Mahaifiyarta
Karanta wannan labarin.
Katanta wannan labarin.