Advertisement

A ƙalla mutane saba in 70 aka kashe a wani harin ƴan jahadi a ƙasar Niger.

A ƙalla mutane saba in 70 aka kashe a wani harin ƴan jahadi a ƙasar Niger.

Hare haren ƴanbindiga sunzama abinda yazama abinda ya zama a kasar Niger a kwanakin baya munkawo muku rahotan kasar Niger wanda yan bin diga suka shiga kasar suka kashe wasu masallata.

A yauma gawani saban rahoto na jinhoriyar Niger wanda rahoton ke nuna.

Harin ya faru ne a kudu maso yammacin ƙasar ta kan iyakar Nijar ɗin da Mali.

Cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da wani magajin gari da kuma shugaban wata rundunar sa kai, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

A yanzu dai ana ci gaba da neman waɗanda suka tsira.

Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki nauyin kai harin.

Waɗanda suka kai harin sun tsere ta iyakar ƙasar da Mali inda rahotanni suka ce sun ɗauke gawargwakin ƴan uwansu da aka kashe.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyyar Nijar ɗin ta kuma ce an yi wa wani ayari ƙarƙashin jagorancin Magajin Garin Banibangou kwantar ɓauna a wani ƙauye da ke da nisan kilomita 55 daga wurin da lamarin ya faru a Yammacin Tillaberi.

Gwamnatin ƙasar dai ta ce wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi kwantan ɓaunar.

Ƴan bindiga dai da ke da alaƙa da ƙungiyar IS na cin karensu ba babbaka a yankin.

Jamhuriyyar Nijar na fuskanatar hare-haren masu i kirarin jihadi a iyakokinta da Mali da Burkina Faso da Najeriya.

Sama da mutum 500 ne aka kashe sakamakon irin waɗannan rikice-rikicen a kudu maso yammacin ƙasar a bana.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari na kasar na kasar Niger.

KU KARANTA WANNAN:

Nayi Nadamar Daukan Cikin Shekau Da Haihuwarsa Saboda Yayi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama Cewar Mahaifiyarsa

Gwamnatin tarayya ta sabunta tsare-tsarenta na kare tattalin arzkin kasarnan na harka internet game da ɓarayin yanar gizo gizo.

Yanzu-Yanzu: Rikici ya kaure tsakanin jami’an ‘yan sanda da Direbobin Keke-Napep dalilin bindige wani mai Keke-Napep da dan sanda yayi

Jarumar Data Janyowa Saratu Daso Zagi Da Tsinuwa Yanzu Ta Sake Sakin Wata Bidiyon

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button