Advertisement

Jaruman kannywood su uku a kasar Saudiyya suna yiwa al’ummar musulma fatan alkairi lokacin da sukeje Umara

Jaruman kannywood su uku a kasar Saudiyya suna yiwa al'ummar musulma fatan alkairi lokacin da sukeje Umara

Shahararraun jaruman masana’antar kannywood suna mika gaisuwar su ga al’ummar musulmai daki daya, a lokacin da suke wajan aikin Umara a kasa mai tsarki Saudiyya.

Wasu jaruman masana’antar kannywood su uku sun ziyarci kasar Saudiyya domin suyi Umara, sannan kuma su roki Allah ya biya musu bukatun su na alkairi.

Cikin jaruman da suka tafi kasad Saudiyya domin suyi Umara sun hada da, Sadik Sani Sadik, Aisha Najamu, Abdul Amart mai kwashewa.

Ga wani dan takaicaccan labari akan wadannan jaruman da suka tafi kasar Saudiyya domin suyi Umara.

Jarumi Sadik Sani Sadik: ficaccan jarumi ne a masana’antar shirya fin-finai ta kannywood wanda yake taka rawar gani, sannan kuma ya dauki lambobin yabo wanda a kwanakin baya aka yi masa shugabancin matasan Arewa.

Abdul Amart mai kwashewa: wanda shine kwamandan kamfen na Yahaya Bello wanda yake bukatar takarar shugaban kasar Nageriya a karkashin jam’iyya mai mulki a yanzu Wato APC, wanda a yanzu haka gwamnan jihar Kogi ne.

Aisha Najamu: Itama jaruma ce a cikin shirin nan mai dogon wanda yake zuwa muku a duk sati wato, IZZAR SO, wanda a cikin shirin ake mata lakabi da Hajiya Hafsa Matawalle, wanda a yanzu ita ma jarumar tauraruwar ta take haskakawa a cikin shirin wanda take burge al’umma da dama saku kallon shirin na IZZAR SO.

Ga hotunan jaruman nan domin a kasar Saudiyya wanda suka dauka su uku lokacin da sukaje Umara.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button