Rundunar ƴansandan Nigeria tayi nasarar kashe ɗaya daga cikin masu karɓar kuɗin fansa yayin karɓar kudi.
Rundunar ƴansandan Nigeria tayi nasarar kashe ɗaya daga cikin masu karɓar kuɗin fansa yayin karɓar kudi.

A ƙoƙarin da ƴansandan Nigeria suke sun cancanta a jinjina musu.
Haƙiƙa kowa yasani irin taɓargazar da masu garkuwa da mutane keyi a fadin wannan ƙasar ta Nigeria ya ta azzara.
Haka zalika ƴansandan Nigeria suna iya bakin ƙoƙarin su don tabbatar da tsaro a fadin kasar baki daya.
A ƙoƙarin da hukumar ta ƴansanda tayi mukuci karo da rahotan dake nuna mana cewa tawagar jami’an tsaron hadin gwiwa a jihar Ekiti dake kudancin Najeriya sun kashe wani mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa a bakin dajin da ke tsakanin Ekiti da Kwara.
Wata majiya ta shaida wa manema labarai a Ekiti tawagar hadin gwaiwa ce ta kashe mutumin, wadanda suka hadarda sojoji da ‘yan sanda da kuma wasu ‘yan banga wanda Sarkin Fulanin Ekiti Alhaji Adamu Abashe ke lura da su.
Jami’an tsaron sun yi kwantan bauna ne a bakin dajin lokacin da aka je biyan kudin fansa da suka kai naira miliyan 2.1 na wani mutum da aka sata, daga nan ne suka bi mutanen da suka je karbar kudin tare da samun nasarar kashe mutumin da ake zargi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda da ke Ekiti Sunday Abutu, ne ya gabatar da gawar mai garkuwa da mutanen a hedikwatar rundunar da ke Ado Ekiti.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari na Ekiti domin jin tabakinku zaku iya biyomu kaitsaye ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Malaman makarantar da aka sace A Jami’ar Abuja rundunar ƴansanda sun sami nasarar cetosu.
Sabuwar Duniya Bidiyan Yadda Wani Ango Ya Kankamai Amaryarsa A Dinnar Bikinsu
Saban matakin tsaro da ƙasar Nigeria ta kawo yasa ƴan kasa baki ɗaya farin ciki.
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.