Saban matakin tsaro da ƙasar Nigeria ta kawo yasa ƴan kasa baki ɗaya farin ciki.
Saban matakin tsaro da ƙasar Nigeria ta kawo yasa ƴan kasa baki ɗaya farin ciki.

Samar da tsaro a kasa yazama dole wa sojojin Nigeria ko ta halin kaka.
Kamar yadda mukasani sojojin Nigeria na fuskantar barazana ta ko ina a fadin kasarnan wannan ne dalilin dayasa suka yunkura wajan wajan tabbatar da tsoro a fadin kasar baki ɗaya.
Wannanne yasa hukumar SojojinNajeriya tafara shirin fara amfani da mutum mutumi masu motsi da jirage marasa matuka wajen tattara bayanan sirri domin fatattakar ‘yan fashin daji da sauran masu aikata laifukan da ke addabar kasarnan.
Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), karkashin Cibiyarta ta Fasahar Mutum-Mutumi mai motsi ta kasa, ita ce tayi hadin gwiwa da rundunar sojojin Najeriya wajen yin amfani da tsarin tattara bayanan sirri na zamani domin magance matsalolin tsaro da suka addabi kasarnan.
Kazalika hukumomin biyu za suyi hadin hannu wajen kera kayan aikin soja da aka kera a cikin gida domin magance matsalar rashin tsaro.
Manufar shirin shine samar da bayanan sirri na farko ga gine-ginen tsaron kasarnan, ta hanyar amfani da fasaha da kuma hanyoyin da ake amfani da su na zamani da nufin kawo karshen barazanar tsaro a kasarnan.
Darakta, Cibiyar Fasahar Mutum-Mutumi mai motsi ta kasa, Engineer Ya’u Garba Isa, shine ya bayyana haka ne a yau a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Sojojin Najeriya da ke Markudi a Jihar Binuwai, Birgediya Janar Yahaya H Abdulhamid a ofishinsa da ke Abuja.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan wannan lamari na tsaro da kasarmu Nigeria ke shirin samar mana dashi a faɗin ƙasar baki ɗaya.
KU KARANTA WANNAN:
Yanzu Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kama Shagirgirbau Jarumin Barkwanci A Kannywood
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwa shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.