Yanzu-Yanzu: tsohuwar jaruma Mansarah Isah ta tabbatar da mutuwar auren ta da Sani Musa Danja

Yanzu-Yanzu: tsohuwar jaruma Mansarah Isah ta tabbatar da mutuwar auren ta da Sani Musa Danja

Tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Mansurah Isah ta tabbatar da mutuwar auren ta ficaccan jarumin masana’antar kannywood Sani Musa Danja.

Auren Mansurah Isah da Sani danja yana daya daga cikin aurarrakin da sukayi karko da dogon zango a cikin masana’antar kannywood.

Daga cikin auratayyar da sukayi karko a masana’antar kannywood sun hada da, auran Darakta Hassan Gigs da tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam, wanda cikin ikon Allah da amincewar sa har yanzu babu wata matsala a cikin wannan auren.

Sai kuma auren jarumi Sani Musa Danja da tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Mansurah Isah, wanda shim duk lokacin da za’a bada misali da airarrakin da sukayi karko a kannywood dole ana sakawa da shi.

Sai dai kuma a halin yanzu kamar yadda wasu suka sani akwai wani abu marar dadi da yake faruwa kuma yake cigaba da faruwa akan auren Sani danja da Mansurah Isah.

Tun lokacin da wadannan ma’auratan suka fara samin sadani anyi cece-kuce sosai akan lamarin, inda wasu suke ganin kamar auren ya mutu wasu kuma suke ganin wani dan sabani kawai aka samu amma auren bai mutu ba.

To a halin yanzu kamar yadda kuka sani Mansurah Isah tana nan tana haska gawurcaccan fim din ta a cinema wato Fanan, inda take ta wallafa hotuna tare da jama’a a wajan kallo shirin.

To a nan ne Mansurah Isah ta wallafa wasu hotuna tare da mijin nata wato Sani danja, inda wallafar da tayi take nuna inda auren nasu ya dosa kamar yadda zaku gani yanzi a cikin bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Kalli shirin LABARINA SEASON 4 EPISODE 5.

LABARINA SEASON 4 EPISODE 5

Karanta wannan labarin.

Rundunar ƴansandan Nigeria tayi nasarar kashe ɗaya daga cikin masu karɓar kuɗin fansa yayin karɓar kudi.

Karanta wannan labarin.

Ango Dan Gwamna Jihar Jigawa Badaru Abubakar Ya Bayyana Ta Kafar Sadarwa Da Suka Hadu Da Amaryarsa Har Ya Aureta

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button