Advertisement

Ƴanbindigar dake ikirarin masu jahadine sunkai wani sumame sansanin sojojin ƙasar Niger.

Ƴanbindigar dake ikirarin masu jahadine sunkai wani sumame sansanin sojojin ƙasar Niger.

Kisan ƴanbindiga yazama saidai addu’a a ƙasar Niger wanda abin tafara tsamari.

A safiyar yaune mukasani wani saban rahoto daga jamhuriyar Niger wanda idan bakumanta a makon da yagabata muka kawo muku rahota dake cewa ƴanbindiga sunkashe mutane saba in 70 a ƙasar Niger ashafinmu na Dalatopnews

Ajiya juma’a rahotan yanuna cewa ƴan bindigar sunkai wani harin sumame a sansanin rundunar sojojin ƙasar Niger.

Wanda a yanzu anshiga fargbar cewa karin wasu sojojin tara sun yi batan dabo yayin harin da yan bindigar da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai kauyen Anzourou.

Ma’aikatar Jamhuriyyar Nijar ta ce maharan sun isa ne a kan motoci da babura, kana suka bude wa sojojin da ke tsaron jama’ar garin wuta.

Wannan na faruwa ne yayin da ake zaman makokin akalla sojojin kasar 70 da masu ikirarin jihadi suka kashe a iyakar kasar da Mali da Burkina Faso.

Ranar Juma’ar da ta wuce ne Jamhuriyyar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu daga yau Juma’a bayan da wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne sun kashe kimanin mutum 70.

Harin ya faru ne a kudu maso yammacin ƙasar ta kan iyakar Nijar ɗin da Mali.

Cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da wani magajin gari da kuma shugaban wata rundunar sa kai, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki nauyin kai harin.

Waɗanda suka kai harin sun tsere ta iyakar ƙasar da Mali inda rahotanni suka ce sun ɗauke gawarwakin ƴan uwansu da aka kashe.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyyar Nijar ɗin ta kuma ce an yi wa wani ayari ƙarƙashin jagorancin Magajin Garin Banibangou kwantar ɓauna a wani ƙauye da ke da nisan kilomita 55 daga wurin da lamarin ya faru a Yammacin jiya.

KU KARANTA WANNAN:

Yanzu-Yanzu: tsohuwar jaruma Mansarah Isah ta tabbatar da mutuwar auren ta da Sani Musa Danja

Rundunar ƴansandan Nigeria tayi nasarar kashe ɗaya daga cikin masu karɓar kuɗin fansa yayin karɓar kudi.

Ango Dan Gwamna Jihar Jigawa Badaru Abubakar Ya Bayyana Ta Kafar Sadarwa Da Suka Hadu Da Amaryarsa Har Ya Aureta

Malaman makarantar da aka sace A Jami’ar Abuja rundunar ƴansanda sun sami nasarar cetosu.

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button