Ku saurari amsar da Sheikh Aminu Daurawa ya bada akan cewa ya halarta mutum ya auri karuwa
Ku saurari amsar da Sheikh Aminu Daurawa ya bada akan cewa ya halarta mutum ya auri karuwa

Idan mace ta shahara da karuwanci sai kuma daga baya ta tuba shin za a iya auran ta, Ko Kuma wani mutum ya shahara da zina shin idan ya tuba za a iya bashi aure.
Akwai wani mutum da suka saba da wata karuwa tun kafin ya musulunta a zamanin jahiliyya, sai bayan musulunci sai suka haɗu da juna sai ta nemi suyi harka sai ya sace mata ya tuba yanzu sakamakon shigar sa musulunci.
To sai ta nemi ya aure ta, sai yace sai ya tambayi Manzon Allah saw akan haka, bayan ya tambayi Manzo SAW, sai aya ta sauka tana haka auran karuwa ko mazinaciya da mazinaci duk wanda aka tabbatar cewa mazinaci ne baya halatta aba shi aure.
Sai ya tuba haka duk wacce aka tabbatar tana zina baya halatta a aure ta sai an tabbatar ta tuba ta gyara halin ta.
Bai halatta mutun ya auri karuwa wacce ta ke tijara da mutuncin ta har sai an sami sharaɗi guda huɗu 4, ga sharudan kamar haka.
(1). Ya zamanto ta tuba daga karuwancin kuma ta yi nadama.
(2). Ya zama ta yi istibra’i, don a tabbatar ba ta da ciki ko wani mai kama da haka.
(3). Ayi gwajin lafiya a tabbatar ba ta ɗauke da wani ciwo da ta samu a wajan karuwancin wanda mijin ya na iya ɗauka.
(4). kuma ya zama akwai wata masalaha a cikin yin haka. kuma ba zai zama surutu da ɓatanci ba a gare su musamman a wajan da aka san ta taɓa yin haka.
Karanta wanna labarin.
Bashin da ake bin jihar Barno da yobe shi yajawomusu akahanasu manfetur a Nigeria.
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.