Duk Duniya babu mutum marar imani marar kunya kamar Baba dan Audu na shirin Labarina, martani daga shafin Rariya Hausa
Duk Duniya babu mutum marar imani marar kunya kamar Baba dan Audu na shirin Labarina, martani daga shafin Rariya Hausa

Duk duniya babu mutum marar imani da rashin kunya kamar baba dan audu na cikin shirin LABARINA mai dogon zango.
Kamar yadda kuka sani shirin Labarina shiri ne mai dogon zango wanda yake zuwa muku a duk sati daga tashar Saira Movies dake kan manhadar Youtube ko Arewa24.
Shirin yana dauke da abunuwan al’ajabi da ban tausayi sannan kuma da wasu halaye da ake nunawa a cikin shirin wanda mutum zai fashimci rayuwar zaman duniya.
Ana kafta cakwakiya a cikin shirin akan wata soyayya da maza uku suke yiwa wata budurwa mai suna Sumayya, wanda suka sanyata cikin dimuwa akan soyayyar da suke mata domin ta kasa ware wanda zata zaba a cikin.
A cikin shirin a kwai wani jarumi a ake kiran sa da Baba dan audu wanda shine ya auri mahaifiyar Mahmud, wanda suka fara soyayya da Sumayya tun farkon shirin Labarin.
To shi dai wannan mutumin mai suna Baba dan audu baya jin kunyar duk wani abu da zaka masa indai zaka biya masa bukatar sa ta hayar bashi kudi.
Wanda har jama’a sun fara yi masa wata fashimta ta daban suna cewa ba shi da imani da shi da kunya, domin a shirin Labarina na wannan satin ya bayyana abubuwan rashin imanin nasa da rashin kuyar da jama’a suke fada a lokacin da Mahmud ya mutu.
Domin ya bayyana wasu halayen sa wanda shi kamar bazai mutu ba wanda har mutane suka fara jin haushin sa duk da abin da yake shirin fim ne, amma hakan yana neman ya bata masa suna har a gaske bama a cikin shirin fim ba.
Kamar yadda jama’a suka fara tsanar Malam tsalaha na cikin shirim Dadin kowa duba da yadda yake nuna halaye irin na munafukai da magulmata, wanda hakan yasa jama’a suka fara jin haushin sa a gaske bama a fim ba.
Bayan an haska shirin Labarina na wannan satin sannan kuma jama’a masu kallon shirin suka ga abin da Baba dan audu yake ya wuce misali, shine har aka fara wallafa hoton sa tare da fadin wasu maganganu a kan sa wanda zasu ita bata masa suna a gaske ba’a fim ba.
Kamar yadda shafin Rariya Hausa suka wallafa hoton jarumi Baba dan audu tare da wani rubutu a kasan hoton nasa, gashi makar haka.
https://www.facebook.com/100057325306600/posts/361492385771602/?app=fbl
Inda suka rubuta cewa: Duk Duniya Babu Marar Imani Kunya Irin Dan Audu Na Shirin Labarin.
Idan Kaine Mai bada Umarnin Film dinnan Ya Dashi.
Hakan yana nuna abubuwan da Baba dan audu yake a cikin shirin na Labarina ba abune mai kyau ba, ya kamata ya sauya halayen sa domin jama’a suka kallon sa a mutum mai kyawawan halaye da kuma nagarta.
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
Karanta wannan labarin.
Wadannan Abubuwan Suna Tasiri Wajen Lalacewar Auren Hausawa A Yanzu Cewar Fauziyya D Suleiman