Duk mace mai yaudara samari Allah ya bata miji mai halin Baba dan audu/Jama’a sun fara bayyana halin Baba dan Audu na shirin Labarina a matsayin mummunan hali

Duk mace mai yaudara samari Allah ya bata miji mai halin Baba dan audu/Jama'a sun fara bayyana halin Baba dan Audu na shirin Labarina a matsayin mummunan hali

Duk mace mai yaudarar samari Allah ya bata miji mai halin Baba dan Audu na shirin Labarina.

Kamar yadda kuka sani Baba dan Audu jarumi ne a cikin shirin Labarina mai dogon zango wanda yake nuna halayen da al’umma suke mamakin, duba da yadda bai saba nuan haka a sauran fina-finan ba.

A cikin shirin Labarina Baba dan Audu ya shahara wajan nuna rashin imani da kauka dai daga abubuwan da zasu janyo jama’a suna masa kallon mutumin banza.

Babu ruwan sa da jin kunya balle ya rike mutuncin sa idan har zaka bawa Baba dan Audu kudi to komai ma zaka iya masa, domin bai damu daka wulakanta shi ba balle ka fada masa maganar da zatasa shi jin kunya.

Haka yake rayuwar sa gaba gadi daga yaje wajan wancan maula sai yaje wajan wancan karbar bashi, har ta kai ga idan ma wani nasa bashi da lafiya bai so ya tashi da wuri domin yana karbar kudaden masu zuwa dubiya, duk a cikin shirin Labarin.

Idan baku manta ba a shirin Labarina na wannan satin Baba dan Audu ya nuna halayan sa karar wanda har aka fara wallafa labarai a kan sa, kamar yadda shafin Rariya Hausa suka wallafa dan wani rubutu a kan sa, kamar haka.

Duk duniya babu marar imani marar kunya irin Baba dan Audu na shirin Labarin.

Idan kaine mai bada umarnin fim din nan ya zakayi da shi.

A lokacin da jarumi Mahmud ya rasu a cikin shirin Labarina a lokacin ne Baba dan Audu ya sake bayyana halayen sa, inda ya nuna halin ko in kula ga rasuwar da Mahmud yayi wanda yana matsayin da a gareshi.

Wanda har takai ta kawo yake danganta rasuwar da lokacin samin kudin sa domin lokacin da yake siyan likkafani ya rage kudi, sannan kuma yake neman cogewa mai motar daya dauko gawar Mahmud kudin sa.

Sannan kuma duk wanda yaje gaisuwa sai ta bayyana masa wasu matsaloli wanda ba tabbas ne akwa su, kama daga rashin abin da za’a ci da dai sauran abubuwan da ake amfani da su lokacin da ake mazan makokin rasuwa.

Zamuso ku ajiye ra’ayoyin ku a sashen mu na tsokaci akan abubuwan da Baba dan Audu yake aikatawa a cikin shirin Labarin mai dogon zango.

Karanta wannan labarin.

An kama Wata Matar Aure Da Saurayinta Bayan Ta Sace Kudin Mijinta Ta Gudu N832,000

Karanta wannan labarin.

Kalli Bidiyon Budurwar Da Take Aikin Karfi Tana Bawa Saurayinta Kudin Domin Ya Aureta

Karanta wannan labarin.

Lalle Duniya Tazo Karshe Yadda Wani Dan Nijeriya Yake Kera Sassan Jikin Dan Mutum, Domin Masu Nakasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button