Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin N-Knownledge Don Tallafa Wa Matasa

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin N-Knownledge Don Tallafa Wa Matasa

Ministar Harkokin Jinkai Agaji Da Inganta Rayuwa Hajiya Sadiya Umar Farouq Ta Bayyana Cewa Gwamnati Ta Soma Wani Sabon Shiri Mai Suna N-Knownledge Domin Tallafa Wa Matasan Nijeriya Su Koyi Aikin Yi A Bangaren Fasahar Zamani

A Wata Sanarwa Da Aka Rabawa Manema Labarai, Babban Sakataren Ma’aikatar Alhaji Bashir Nura Alkali Ya Bayyana Cewa An Fara Shirin Ne A Dukkan Sassa Shida Na Kasarnan Tare Da Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja Kuma Wani Bangare Ne Na Shirinan N-power

Alkali Yace N-Knownledge Wani Bangare Ne Na Shirin N-power Wanda Zai Maida Hankali Ga Baiwa Matasan Nijeriya Horaswar Da Ta Kamata Tare Da Satifket Domin Su Zama Kwararrun Ma’aikata Masu Kirkira Kuma Yan Kasuwa Da Zasu Iya Yin Aiki A Cikin Gida Da Kasar Waje

Shirin Na N-power (N-knownledge ) Zai Horas Da Matasa 20,000 Daidai Da Muradin Duniya A Matsayin Wadanda Zasu Iya Yin Aiki A Kasashen Waje A Bangaren Fasahar Harkokin Komfuta Da Intanet .

Babban Sakataren Yace An Tsare Bangaren Horaswa Na Shirin Ne Don Bunkusa Kwarewar Matasan Wajen Kirkira Manhaja Da Horaswa Kan Hadawa Da Gyara Kayan Aikin Komfuta Wanda Zai Sanya Nijeriya Ta Shiga Sahun Kasashen Dake Tura Ma’aikata Zuwa Wasu Kasashen Domin Su Yi Aikin Hada Manhaja

A Cewarsa Shirin Zai Samar Da Kwarewa Da Iyawa A Fagen Tsara Manhajojin Wayar Hannu Da Gina Gidajen Yana Yare Da Inganta Basira Don Habaka Masana’antar Fasahar Yada Labarai Da Ilimin Intanet A Nijeriya

Shirin Ya Kunshi Aje Matasa Wani Kebebben Wuri Ana Hiras Dasu Har Tsawon Wata Uku Sannan A Basu Aikin Wucin Gadi Na Wata Shida A Dukkan Sassa Shida Na Kasarnan

Inda Daga Karshe Ya Bayyana Cewa Dukkan Matasan Da Aka Hiras Dasu Za’a Basu Takardar Sheda

Ku Kara Karanta Wannan Labarin

shagalin da ƴa Kungiyar ISWAP tayi bayan naɗa Sani Shuwaram, mai kimanin shekara 45 a matsayin sabon shugabanta na yankin Tafkin Chadi

Lalle Duniya Tazo Karshe Yadda Wani Dan Nijeriya Yake Kera Sassan Jikin Dan Mutum, Domin Masu Nakasa

Masu Karatu Bayan Kun Saurari Wannan Rubutun Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sagen Mu Na Tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button