Jarumar Hollywood dake Amurka ta kira wasu kasashen musulmai jahilai sabida sunki yarda a haska wani fim dinta wanda ake auren jinsi a ciki

Jarumar Hollywood dake Amurka ta kira wasu kasashen musulmai jahilai sabida sunki yarda a haska wani fim dinta wanda ake auren jinsi a ciki

Ficacciyar jarumar fina-finan Amurka mai suna Angelina Jolie ta tayi zazzafan martani ga kasashen musumai akan sun hanata haska wani sabon fim din ta wanda aka fitar a kwanakin nan.

Inda jarumar ta kira musulmai jahilai dalilin sun hana haska fin din nata na kamfanin Marvel, sabida a cikin fim din nata ana bada goyon bayan auran jinsi sannan kuma ana nunawa.

A fim din nata ana nuna yadda wasu mutane jinsi daya suke sumbatar junan su inda aka kaddamar da haska shirin a wasu kasashen musulmai da suka hada da, Kasar Saudiyya, Qatar, Kuwait, Bahrain, Oman.

A kwanakin baya ne wata hukumar tace fina-finai ta umarci kamfanin Marvel daya yanke wasu wurare da ake nuna abubuwan da basu dace ba a cikin fim din, sai dai kamfanin yayi kunnen uwar shegu da wannan umarnin da aka bashi.

Anjelina Jolie wacce ta fito a matsayin Thena Abadi a cikin fim din ta fadi albarkacin bakin ta game da al’amarin, a wata shira da akayi da Angelina Jolie ta bayyana al’amarin a matsayin marar dadi, sannan kuma ta kira kasashen musulman da suka hana haska wannan fim din a jahilai. Kamar yadda Labarun Hausa da Nbcnews suk ruwaito.

Karanta wannan labarin.

Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun kwace wasu kauyuka a jihar Sokoto tare da nada wasu daga cikin su shuwagabannin kauyukan

Karanta wannan labarin.

masu garkuwar sun bukaci a basu buhunan shinkafa da galan-galan na man gyada don su sami abincin ciyar da mutanen da suka sace a coci.

Karanta wannan labarin.

Kai Tsaye Tattauna Da Aminu Saira Kan Mutuwar Mahmud A Cikin Shirin Findi Labarina Mai Dogon Zango

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button