mummunan harin ƴan fashin daji, da ya yi sanadin kashe kimanin mutum shida.

mummunan harin ƴan fashin daji, da ya yi sanadin kashe kimanin mutum shida.

Yankin Zamfara na cikin tashin hankali da fargabar ƴanbindiga.

Kamar yadda mukasani yakin Zamfara na cikin yankunan dake fama da yan bindiga da fashin daji a cikin jihar ta Zamfara.

Wasu rahotanni daga mazaɓar Rijiya, kudu maso gabas daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara na cewa al’ummar garin sun kwana cikin makoki bayan wani mummunan harin ƴan fashin daji, da ya yi sanadin kashe kimanin mutum shida.

Wani mazaunin garin ya ce da tsakar rana maharan suka aukowa Rijiya a kan babura, da harbe-harbe, har ma suka sace matan da har yanzu ba a iya tantance adadinsu ba.

Ya ce akwai mutanen da ke kwance asibiti da suka ji rauni a harin, kuma daga cikin waɗanda maharan suka tafi da su har da yara ƙanana.

Zamfara na fama da hare-haren ƴan fashin daji duk da matakan da hukumomi suka ɗauka ciki har da rufe layukan sadarwa a sassan jihar.

Da dakatar cin kasuwannin mako-mako da sauransu.

Mutanen yankin suka ce ‘yan fashin daji sun addabesu saboda rashin jami’an tsaro da suke fama dasu a yankin nasu.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin akan wannan abun da yake faruwa a yankin Zamfara domin jin tabakinku a sahinmu na tsokaci.

KU KARANTA WANNAN:

Dogon Beni Daya Kashe Mutane A Lagos, Ashe Saɓon Allah Sukayi Shiyasa Hakan Ta Faru

Tirkashi: An gano wani boyayyan al’amari da yasa ‘yam matan hausawa suke yin bilitin tare da shan kwayoyi da yin allura

Mutuwar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din LABARINA Yanzu Akayi Cikakken Bayani Akan Mutuwar Tasa

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin N-Knownledge Don Tallafa Wa Matasa

Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button